Menene Fyade da illolin aikata shi a cikin al’umma?

Menene Fyade da illolin aikata shi a cikin al’umma?
Menene Fyade da illolin aikata shi a cikin al’umma? 


Assalamu alaikum wa rahamatullahi ta’ala wa barakatuhu. Insha Allah yau na zo muku da bayani kan al'amarin da ya zama ruwan dare cikin al'umma. 


Menene Fyade? Fyade dai na nufin aikata ko saduwa da mace ko namiji, ta amfani da hanyar karfi, ba tareda amincewar dayan bangare ba. Fyade yakan iya faruwa namiji ya yi wa mace, ko ita mace ta yi wa namiji, ko yanzu da zamani ya lalace, namiji ya yi wa namiji ko mace ta yi wa mace. Ba shakka wannan mummunan aiki ne da ba addini ko al’ada da suka aminta da shi ba.


Nau'in Fyaɗe (ire-iren Fyaɗe) 


Fyade yanada nau’ukansa kamar haka:


1) Fyade na kai tsaye; Wanda galibi yakan faru ne tsakanin mutane da wata kila ba su san da juna ba, haka kawai namiji zai ji ya kwadaitu da mace ko ita ta ji haka, sai fyaden ya auku.


2) Fyade tsakanin masoya; Wannan nau’in yana faruwa ne tsakanin masoya da suka shaku da juna, wata kila ma sukan sadu a tsakaninsu, amma kasancewar yanayi na ita ta hana shi ko shi ya hana ta sai fyade ya auku tsakaninsu.


3) Fyade na abota ko shakuwa; Wannan yakan faru ne a tsakanin mutane da suke a unguwa ɗaya, wata kila kan yanayi na shigar mace har ya sa a ji ana so a mata fyade kasancewar ana wuri daya ana kallon motsinta


4) Fyade tsakanin ma’aurata; Wannan yakan faru ne tsakanin ma’aurata inda miji zai danne matarsa da karfi domin ya biya bukatarsa, musamman idan ita matar batada bukatar hakan a lokacin. 


5) Fyade na taro; Wanda aka fi sani da gang rape, shi wannan fyaden mutane da dama ne za su taru kan mace daya, ko wannensu ya yi amfani da ita, galibi irin wannan fyaden har rasa rayuwa ake yi.


Laifin Waye ke jawo haddasa fyaɗe? 


Kai tsaye ba za mu iya ayyana wasu al’umma muce laifinsu ne ba kan fyade da ke faruwa, amma ba shakka faruwar fyade a cikin jama’a akwai laifi na wasu:


Iyaye; Sau da yawa bahaushe kan ce, “sadaka daga gida takan fara” iyaye musamman mata, su tarbiyyar mata take a hannunsu, su ake tunani su san shiga da fita na ‘ya’yansu mata, saboda galibi yanzu fyade ya fi aukuwa kan mata ne. amma sai ka ga uwa yarinyarta budurwa ta fita tun safe ba za ta neme ta ba har dare lokacin yarinyar za ta dawo, ina taje, oho! a ina ta ci abinci, oho! wasu ma sai ka ga ba a gida suke kwana ba. 


A bangaren kananan yara kuwa, sai ka ga uwa ta bar yara kanana mata suna fita ba ko wando a jikinsu, a haka za su dinga gararanba kan titi da lunguna suna wasa cikin yara suna giftawa gaban miyagun unguwa, kafin uwa ta ankara ankai ta anbaro, sai ta dawo dora hannu bisa kai, bayan tun farko laifinta ne. Laifin uba anan shi ne, an ji ya fita aiki ko neman abinci, idan ya dawo me yasa ba ya bincikar wanne hali yaran nasa suke ciki? Ko ya dinga dan dawowa daga wurin aiki domin duba yanayin gidansa. Gaskiya ni a wurina laifin iyaye ne ta 98%.


Gwannati; Dimokuradiyyance, an ce gwannati an kafa ta ne domin ta kare hakkin duk wani dan kasa nata, idan haka ne kuwa yanada kyawu a tarar a kowacce unguwa akwai tsaro daga gwannati ta yadda fyade zai ragu a cikin al’umma, amma gaba daya gwannati hankalinta ya karkata kan cika aljihunta da lasawa bakinta abu mai dadi, wanda ba karamar barazana ba ce a tsaro na kasa ma baki daya.


Yaran Da Ake Yi Wa Fyaɗe; Wani/ta za su yi mamaki idan nace da laifin yaran da ake yi wa fyade, idan muka duba yanzu zamani ya yi lalacewar da wasu dunki da ake yi, gaba daya sai ka ga jikin mace ya bayyana kama daga nonuwanta har kira ta kunkurunta, wanda kai tsaye idan cikakken namiji ya kalla zai ji ya kwadaitu, hakan kan janyo fyade ya aiku. Wasu yaran sukan yaudari samari sosai, su kuwa samarin domin ramuwa kan yaudara da aka yi musu, sai ka ga sun yi wa yarinya fyade. Wasu matan kuma su da kansu ke kai kawunansu a dakin samari. Wasu matan kuma shaye-shaye suke yi wanda zai sa su fita hayyacinsu, sanadiyyar haka, sai ayi musu fyade.


Dattijawa Da Mutanen Unguwa; Idan iyaye sun yi sakaci, gwannati ta kasa, bai dace mutanen unguwa suma su koma ‘yan kallo ba, ba shakka mutanen unguwa dole suna ganin abubuwa da ke wakana a unguwanni, tun daga fita da mata ke yi na banza da sauransu, da za su tsawatar da tun jimawa abu ya ragu. Don haka Sunada laifi suma


Illolin Fyaɗe 


Mun ji bayani kan menene fyade? Yanzu kuma za mu yi bayani daga cikin illolin sa kamar haka;


Kamuwa Da Cuttuttuka; Galibi masu yin fyade za ka tarar suna yin holewarsu a gefe, wasu ma sai a tarar suna dauke da miyagun cututuka irin HIV ko STDS. Sai kuga an sakawa wadanda aka yi wa fyaden ba su ji ba ba su gani ba. Hakan ta sha faruwa


Samun Rauni; Kasancewar da karfi ne ake yi wa mace ko namiji, a yayin aikatawar wasu akan ji musu da rauni sosai, wasu a al’ura har jini ya dinga fita musamman yara kanana, wasu kuma a jikinsu ake ji musu da ciwon.


Rikita Mutum Da Fitar Da Shi A Hayyacinsa; Wasu da ake yi wa fyade, sai ka ga har abin ya taba kwakwalwarsu, wasu ma sukan sami tabin hankali da makamantansu.


Zubar Mutuncin Shi Wanda Ya Aikata Fyaɗen; Duk wanda aka ce ya taba yin fyade, za ku ga mutuncinsa ya ragu a idanun mutane zai zamo abin gudu kuma abin kyama, wanda har zuri’arsa ba za su tsallake abin fada ba kan fyaden.


Shafawa Wanda Tsautsayin Ya Far Wa Tabo; Wasu suna rike mata da yawa da wannan tsautsayin ya far wa, bacin ba laifinsu ba ne, amma a haka wasu har ba’a ake musu, wasu kuma ana musu dariya da nuna musu kyama. Wanda sam bai dace ba.


Kawo Zuri’ah Da Ba Ta Dace Ba; Ta hanyar fyade akan samu ciki ya shiga har a haihu, wanda ta sanadiyyar haka yaro ya tashi cikin zuriah ga shi ba wanda ya san mahaifinsa.


Raba Aure; Wasu mazajen idan aka yi wa matansu fyade, sai ka ga sun rabu da su. 


Hana Aure; Wasu kan wannan tsautsayi ya far musu sai ka ga kowa na gudun ya aure su, wasu ma daga karshe dole tsaran kakansu ne za su aura.


Abubuwan dubawa a sillar aikata wannan mummunar ɗabia ta Fyaɗe wato Rape abubuwane guda biyu ne 


1.Tsautsayi da mummunar ƙaddara: za kaga wani lokacin yarinya kawai an aiketa sai a tareta a hanya ai mata toh wannan dole zamu kirashi da tsautsayi da mummunar ƙaddara.


 2. Sakacin iyaye: Yawancin lokaci wallahi bakwa bina bashin rantsuwa sakacin iyaye shi ke janyo a yiwa yara fyaɗe, sai kuma a zo ana cewa kaddara ne, misali kinada ɗiya mace ya kamata kullum kina tare da ita, a'a sai ki aiki almajirinki yaron gida kai wani lokacinma babban danki namiji sai kice ya dauketa ya tafi da ita, kan wane dalili? kinsan ba za ki kula da ita ba wa ya sa ki haifar ta. Ko kuma kina cikin gida ki bar yarinya ba pant ta fita waje ko a jikinki saboda saka ci, wallahi mata muma sai mun gyara.


Menene ke haddasa fyade? 


Daga cikin abubuwan da suke haddasa fyade, akwai;


1- Sakacin iyaye; Akwai iyaye wanda zaku ga suna barin kananan yaransu fita barkatai, duk yanda ransu yake so. Abu ne wanda ya yawaita yanzu, musamman ma mutanenmu na kauyuka. Sau da dama zaku ga yarinya ta fita babu kaya a jikinta, sai an yi sa'a ne za'a ganta da pant.


Wannan abun na daya daga cikin manya-manyan abubuwan da suke haddasa yin fyade ga kananan yara. Saboda akwai da dama maza wanda suke da karfin shaawa, ba wai ga manyan mata kawai ba, har ma ga kananan yara.


2- Shigar tsiraici da ta yawaita ga ƴan matan yanzu. Wasu ƴan matan sai su saka tufafi wanda duk ilahirin kirarsu a bayyane take, hakan kuma zai iya sakawa wani namiji ya hadiyi yawu a kanta, kuma ya san bashi da halin mallakarta a matsayin matarsa, dan haka sai ya bi hanyar da yake ga kamar zata fi masa sauki domin magance damuwarsa.


3- Biye-biyen bokaye


Da dama wasu mazan bokaye ne suke basu asiri su ce dole sai sun samu kila wata mahaukaciya sun mata fyade, kafin asirin ya yi tasiri.


4- Wulakanta maza da mata ke yi; Wata macen yar wulakanci ce, babu damar namiji ya ce yana sonta sai ta wulakanta shi, ko wannan zai iya ja ya yi aniyar rama wulakancin da ta masa, ta hanya mafi ciwo, wato ya mata fyade.


5- Yawaita karatu ko kuma kallon abubuwan da zasu tayarwa mutum sha'awa. Shima yana taimakawa wajen cire tunanin aikata fyade. A nan ba wai ina maganar mace ko namiji ba. Saboda shi fyade har mace ma zata iya yi wa namiji.


Dan haka matsawar suka yawaita karanta batsa, ko kuma kallon batsa, a ko wane lokaci shaawarsu zata iya tashi, wadda zasu kasa controlling din kansu, a karshe su tari duk wanda Allah ya hada su da shi kawai su masa fyade.


Mafita daga rage yawaitar fyade


Bayan jin bayani kan menene fyade da illolinsa ga al'umma, sai bayani kan menene mafita?


Mu kanmu sai mun tarbiyyantu mun gane cewa yara fa amana ce Allah ya bamu kuma zai tambayemu gobe kiyama. Kamata yayi yarinyarki tana jikin ki koda yaushe kinayi kina yi mata gyara kina molding dinta yanda kikeso ta kasance a cikin hikima.


Muguji bawa almajirai, makota, maza in general yaranmu dan ba ƙaramar fitina bace. Sannan gyara ba kawai sai akan danka ba iya gwargwadon yanda zaka iya ka taimaka a makoda or the society at large. Allah ya Kare mana zuria. 


Ba sai na tsaya yin dogon bayani game da miye shi karon kanshi fyaden ba, saboda kusan yanda muke nan, babu wacce bata san menene fyade ba. Kai tsaye zan fada a kan bayanin abubuwan da suke haddasa shi, illolinsa da kuma hanyoyin magance sa (mafita)


Daga cikin mafita kan rage yawaitar faruwar fyade akwai;


Addu’ah, ita addu’ah takobin mumini ce kuma ba ta faduwa kasa banza


Iyaye su dage su san cewa ‘ya’yansu hakki ne a kansu, kuma idan basu kula da tarbiyyarsu ba wallahi ubangiji zai tambaye su gobe kiyama


Gwannati ta dage wurin ganin ta saka tsaro domin dakile wannan mummunar akida, haka ta dage wurin ganin an hukunta duk wanda aka kama da wannan laifin, a kuma kafa kwamiti da zai dinga yawatawa yana fadakar da mutane illar fyade da bayar da misalai, a kuma kafa kwamiti da zai dinga kulawa da wadanda tsautsayin fyade ya farwa.


Mutane su daina kyamar wadanda tsautsayin fyade ya farwa, domin hakan kan janyo matan su shiga uwa duniya.


Mutanen unguwa su kafa kwamiti da zai ba wa unguwanninsu tsaro, su dinga lura da masu shiga da fita a unguwanninsu.


Yara su ji tsoron Allah su dinga amfani da abinda ake karantar da su a islamiyya, su dinga shiga irin wacce musulunci ya tanadar.


A dinga yi wa mazaje aure idan aka lura ba za su iya kame kawunansu ba.


Allah yaimana jagora




Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post