Menene ciwon asthma? - Android Pols - latest news, natural remedies, and entertainment

Menene ciwon asthma?

Menene ciwon asthma?
Menene ciwon asthma? 


Asthma ciwone da yake samun halittar da take bawa mutum damar numfashi wato huhu (lungs).


Idan mai Asthma ya shaqi baqon abunda yake tayar da ciwon, shi kuma wannan abu ya samu damar shiga huhu, to sai ya fara qoqarin toshe qofofin da iska take shiga ko fita,sakamakon haka sai hallitar wurin ta fara qanqancewa (constriction) a qoqarin ta na bada kariya.


A saboda shigar wannan baqon abu (irritants) zai saka wurin numfashi ya fara kumbura (Inflammatory response)sakamakon reaction.


Wannan kumburin zai samar da fitar ruwa a matsayin majina duk wurin qoqarin bada kariya ga naman huhu.


Sanadiyar qanqancewar qofofin numfashi, da taruwar majina da kumburin huhu hakan sai ya haifar da ciwon qirji, matsalar shaqa da fitar numfashi da sauran alamomin ciwon Asthma.


MENENE ALAMOMIN CIWON ASTHMA? 


-Shortness of breathing shine mutum yaji shaqar iska na masa wahala ko kuma iskar da yake shaqa yaji tayi qaranchi.


-Chest tightness daurewa, matsewa ko kuma ciwon qirji.


-Increased Mucus production, Yawaita samar da majina a sakamakon matakin bayar da kariya da huhu yayi.


-Rapid breathing shine saurin yin numfashi a qoqarin jiki na samar da iska da tayi qaranchi.


-Tari


-Difficulty in sleeping, Kasa yin bacci sakamakon qaranchin iska da tari hakan na hana mai ciwon Asthma samun bacci yadda ya kamata.


-Wheezing shine fitar da wani sauti lokacin numfashi saboda toshewar da aka samu sakamakon yawan ruwa da majinar da ya taru a qirji.


Amb(Nr)Sumayya Ibrahim Sa'ad 

RN,RM,PND



Related Posts:
Previous article
Next article

Leave Comments

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel