Menene Blockchain |
"Blockchain Fasaha ce ta ilimin computer dake amfani da lissafin algorithm wajen tattara bayanai da rarraba su zuwa kan "Nodes" wato Computoci kai tsaye (Decentralized) ba tare da wani mutum ko wasu mutane sun tsaya a tsakiya ba (Middlemen ko Central Authority), dukkan abinda aka aiwatar na hada-hada yana taruwa ne akan dukkan Computocin da aka 'dora su akan tsarin a duniya, babu wani waje 'daya (Database) da ake ajiye bayanan, dukkan ayyukan da ake yi akan Blockchain ana amfani da ilimin Cryptography ne".
Tamabayoyi sun yi yawa kan Menene Blockchain? ~ Blockchain tsarin rarraba bayanai ne zuwa kan Computocin a bayyana ne, shine abinda ake kira da "Distributed Ledger System or Technology" ko "DLT" a takaice.
~A cikin blockchain a galibin lokuta baka bukatan izini, umarni, amincewa ko sahalewar kowa kafin ka fara amfani dashi, ka'idojin computer din ne kawai zaka cike, da zaran ka cike za kayi amfani dashi daga ko'ina a duniya. Shine "Permissionles" da kake ji ana magana akai.
~ Shi blockchain Fasaha ce ta ilimin rarraba bayanai kai tsaye (Decentralized System) akan internet da Computer, abinda ake nufi da Decentralized a nan shine kai tsaye, wato babu wata hukuma ko wasu mutane da suke da iko akan duk abinda ake yi akan Blockchain domin Decentralized System ne, domin fahimtar haka, sai mun tuno da menene Centralized system, misali:
~ Kana da Kudi a GT Bank, kana da Account dasu kenan, bayanan ka, sunan ka, hoton ka, shekarar haihuwar ka, da yawan Kudin da kake dashi, duk an ajiye su ne akan Database na Computar Bankin, ana iya aikewa da Kwafin (Copy) din bayanan zuwa CBN, NDIC da sauran hukumomi, wadannan bayanan naka idan anyi hacking din Database din Bankin ka toh akwai tashin hankali.
~ Domin bayanan suna kan Database din Computar Bankin ne kadai, a Blockchain bayanai suna kan Computoci ne da Allah kadai yasan yawan su, idan ana so a lalata bayanan dake kan Blockchain sai dai a nemi wadannan Computocin gaba dayan su daga ko'ina a duniya idan za a iya kenan.
~ Idan ka bude Facebook ko Email zaka Saka Lambar wayar ka, da bayanan ka, wadannan bayanan suna taruwa ne a cikin Rumbun Adana Bayanai ko Database na Facebook da Email, babu inda zaka same su sai in kana da ikon ganin Database din su, su Facebook da Email din kenan.
~ Kamar Ahmadu Bello University Zaria, idan ta tattara bayanan 'daliban ta sai a ajiye su akan Database na hukumar makarantar a internet, babu me gani sai su, babu mai iya gyara kuskure akai sai su, babu mai gogewa sai su, wannan shine Centralized system kenan.
~ Idan aka yi Kutse a cikin "Rumbun Adana Bayanai" wato aka yi hacking Database din za'a iya sace bayanan, za'a iya Canza su, ko a goge su gaba daya su zama kamar ba'a yi ba. Yayin da hakan ba zai yuwu ba akan Blockchain, saboda baka San yawan Computocin da suke dauke da bayanan a duniya ba, idan aka lalata bayanan dake kan Computer guda daya da take da bayanan wannan Blockchain din, toh ya za'a yi da sauran Computocin dake fadin duniya?
~ Shi ma blockchain Database ne, amma "Open distributed ledger", a bude yake, kuma yana rarraba duk abinda ake yi na hada-hada akan sa, baya ajiye bayanai a waje 'daya. Ba kamar Centralized system na Bankin ka ba, wanda ake tura bayanan ka zuwa waje 'daya, wato zuwa cikin "Rumbun Adana Bayanai" wato "Database" na Bankin ka.
~ A cikin blockchain kowa yana ganin abinda ake yi, babu wanda yake da ikon rufewa ko canzawa ko dakatarwa domin daga ko ina a duniya Computoci suke aikin, kuma suke ajiye bayanan abinda aka yi.
Menene Blockchain? Me yasa ake kiran Blockchain da Kalmar "Block" da "Chain"?
Dalili shine saboda bayanan transactions ko hada hadar da ake yi akan Blockchain suna zuwa ne a warwatse sai tsarin wato "Protocol" din sai ya dinga hada su waje 'daya kadan-kadan kamar Blo ko Block, sai ya dinga jera su kamar jerin Sarka (Chain) daga wannan sai wancan, daga wancan sai wancan a jere haka, shine "Block Chain".
~ Kowane block yana ɗauke da bayanan hada-hada ne da aka yi a wani lokaci da ya gabata, idan za ayi sabon block dole sai ya dace da asalin yadda tsarin block na farko akan wannan Blockchain din yake, wato sai ya dace da "Genesis Block".
~ Idan bai dace dashi ba toh Computocin za su buge shi su watsar dashi, ba za su yarda ba, saboda bai zo da Mathematical calculation ko Mathematical Puzzles irin wanda yake a asalin blockchain din ba tun na ranar farko, shiyasa zaka ji masu CORE Blockchain suna cewa "CORE DAO In Math We Trust", wannan mathematics din suke magana akai, saboda babu karya a Mathematics ba yaudara, basu yarda da kowa ba sai Math.
~ Idan kayi yunkurin shigar da wani tsarin calculation don kirkirar sabon block akan Blockchain wanda ba irin nasa ba toh ba zai karba ba, idan ka shigar da wanda ya dace kuma toh kowace computer a duniya zata mallaki wannan bayanin.
~ Idan kowace computer ta mallaki bayanin toh ba zaka iya yin komai na cutarwa akan Blockchain din ba. A cikin sha'anin Blockchain ba lallai ne ka yarda da mutumin da kake Hulda dashi ba, shin yana da gaskiya ko baya da ita? shin mai Amana ne ko mayaudari ne, baka bukatan wannan, domin zallan Mathematical calculations ne kawai suke aiki akan dubban Computoci, shine zaka ji ana cewa "Trustless system".
~ Wato an mika aiyukan a hannun Computoci da mathematics tunda ku mutanen baku da gaskiya yanzu, baku yarda Al-Qur'ani da Sunnah su daidaita ku ku yi gaskiya ba.
~ Kowane Block dake dauke da bayanai akan blockchain yana dauke da wasu abubuwa uku kamar haka:
1. Data.
2. Nonce.
3. Hash.
Za muyi bayanin su a rubutu na gaba, in sha Allah.
~ A cikin blockchain akwai "Transparency" shine dai daito, duk abinda ake yi dai dai da dai dai ne, abinda yake kan wannan computer shi yake kan wancan, abinda ka duba ka gani shine irin abinda nima idan na duba zan gani, babu rufa-rufa a ciki, hatta wadanda suka yi Blockchain ba zasu iya boye komai akai ba.
~ Ba kamar Rumbun Adana Bayanai na Bankin ka ba (Database), sai an nuna maka zaka gani, babu wanda yake da copy din bayanan sai su kadai. Idan aka yi rashin sa'a hackers suka yi Kutse sai dai Allah ya tsare kawai.
~ Kuskure ne kayi tunanin cewa wai Crypto Currency kawai ake yi da Blockchain, No, No, No, ko kadan. Crypto Currency wani 'dan karamin abu ne a cikin Blockchain, kamar jihar Bayelsa ce mai local government 8 da mutane dubu Dari 500k a saka ta a cikin jihar Kano mai local government 44 da mutane kusan Miliyan 20.
Menene Blockchain?
~ Blockchain ana amfani dashi wajen harkar lafiya, magance rashin tsoro, Siyasa zabe Mai inganci, harkar kasuwanci, samar da receipt da ajiye bayanan da har abada ba za'a goge su ba, kamar ajiye Al-Qur'ani da manyan littattafai masu muhimmanci wadanda ake jin tsoron nan gaba za'a iya bata su ko gurbata su.
An fara tattaunawa akan fasahar Decentralized Blockchain a farko farkon 1990s har zuwa wajen 1997. Sai a 2009 aka samar da Blockchain na farko a duniya, shine Bitcoin Blockchain. Wanda wani mutum da ba asan fuskar sa ba ya samar da Bitcoin Blockchain, shine "Satoshi Nakamoto", me yasa ya boye fuskar sa?
~ Saboda wannan fasahar ta Blockchain karfin ta yayi yawa, hikimomin dake cikin ta yayi yawa, idan Gwamnatocin kasashe suka san fuskar sa sai sun hallakar dashi, kafin su hallakar dashi kuma sai an nemi ya rusa wannan abun idan zai iya, wanda shi kansa ba zai iya ba.
~ A yanzu a hakan da ba'a san fuskar Satoshi Nakamoto ba Gwamnatocin kasashe suna ta fada da Crypto Currency, yayin da suke cewa basa fada da Blockchain, domin Blockchain yana dauke da alkhairai masu yawa, sai dai suna fadin haka ne don sun gagara kawo karshen fasahar Blockchain.
~ Tare da cewa wasu suna fahimtar cewa sunan Satoshi Nakamoto suna ne da wasu Injiniyoyi suka buya a bayan sa, sune suka kirkiri Bitcoin ba wai wani mutum ɗaya ba. Amma anyi ittifaqi cewa sunan Satoshi Nakamoto sune na na 'yan kasar Japan.
~ Kasashen da suke ganin Bitcoin zai karya Darajar kudaden su da fallasa asirin su sai suke yakan Bitcoin amma galibi Bitcoin da Blockchain din gaba daya ne basa so. Da yawan kasashen duniya sun sadaukar yanzu, sun mika wuya ba zasu iya dakatar da fasahar ba, sai suka koma cewa to a kawo gyara a cikin sa ta yadda ba za'a dinga cutar da mutane dashi ba ko boye kudaden ta'addanci da Miyagun Kwayoyi da Kudaden safarar Mutane da sauran laifuka.
~ Blockchains da suka biyo bayan Bitcoin sune irin su Ripple (XRP) da Ethereum Blockchain, Ethereum akan sa aka fara samar da Smart Contracts da Decentralized Applications.
~ Polygon Blockchain, Matic Blockchain, CORE Blockchain, RENEC Blockchain da sauran su.
Zamu tsaya a nan, amma nasan akwai tambayoyi.
1. Menene Cryptography?
2. Menene Database?
3. Shin za iya hacking Blockchain?
4. Yaya ake yin bincike aga abubuwa dake gudana akan Blockchain?
5. Tunda ance Blockchain ana ganin komai, babu sirri a cikin sa kenan ko yaya?
6. Menene Ethereum Virtual Machine (EVM).
7. Su menene EVM compatible Blockchains?
8. Menene Private Blockchain? Me ya bambanta Private Blockchain da Public Blockchain irin su Bitcoin Blockchain, CORE Blockchain, Ethereum, RENEC da sauran su?
Da sauran bayanan zamu dinga kawo su kadan-kadan a rubuce, ba zamu dinga tsawaita rubutun kamar wannan ba, in sha Allah. Ina fatan dukkan mai yin tambaya a kan Menene Blockchain? Yanzu ya fahimta ya ilimantu, Allah yasa mu dace.
Abdul-Hadee Isah Ibraheem.