Menene Alamomin Raunin Mazakuta? - Android Pols - latest news, natural remedies, and entertainment

Menene Alamomin Raunin Mazakuta?

Menene Alamomin Raunin Mazakuta?
 Menene Alamomin Raunin Mazakuta? 


Raunin mazakuta abu ne dake addabar mazaje sosai, aure da dama ya mutu a dalilin rashin Æ™arfin mazakuta, idan namiji bashi da Æ™arfin gabansa akwai babbar barazana a zamantakewar aure. 


Menene alamomin raunin mazakuta? Wadanne alamomi ne mutum zai ji ya fara tunanin yana da matsalar raunin mazakuta?WaÉ—anan sune tambayoyi da muke samu daga mazajen aure. Don haka ga wasu daga cikin alamomin raunin mazakuta kamar haka;


1.  Rashin Mikewar Azzakari; Haka na faruwa ko da an yi tunanin jima'i ko kuma ma an samu haduwar jikin mace da shi mai matsalar.


2.  Saurin Kwantawar mazakuta; Abin nufi anan azzakarin zai mike sai dai ba da jimawa ba, sai ya kwanta, tun kafin aje ga saduwa ko kuma da zarar an fara. A lura wannan na da banbanci da saurin kawowa, saboda anan za ta kwanta ne ba tare da mai matsalar ya kawo ba.


3. Rashin Sha'awa; Mai wannan matsala zai ji ba ya sha'awar saduwa da iyali. Ma'ana gaba daya sha'awarsa ta gushe.


MENENE ABUBUWAN DA KE HADDASA SAURIN INZALI / KAWOWA? 


Haryanzu dai babu wani sahihin bayani ko dalili dake bayyana dalilin saurin kawowa ba, sai dai wasu bayanai akan dalilan da ka iya bada haske gameda matsalar saurin kawowa ga maza (premature ejaculation). Sune kamar haka:


1. Matsalar raunin mazakuta  (erectile dysfunction). Idan namiji baya da karfin gaba to akwai yiwuwar a sami saurin kawowa lokacin jima'i, haka kuma,  idan akwai karfin zakari to akwai yiwuwar dadewar yin jima'i mai tsawo tsakaninin ma'aurata biyu. Saboda haka, saurin inzali na iya zama wani lokacin alama ce ta raunin mazakuta.


2. Yanayin halittar wasu mazajen. Wani haka Allah Ya halicce sa ko minti 1 baya iya yi da mace. Amma wannan baya nufin baza'a iya samun saukin yanayin ba. Za'a iya neman magani ko Allah Yasa a dace.


3. Samuwar hadari (accident) wanda zai iya shafar al'aurar mutum. Hadari wanda ya shafi lafiyar al'aura na iya haddasa matsalar saurin kawowa.


4. Magungunan kayan mata/da'a da mata keyi. Magunguna na matsi da mata ke sakawa cikin gaba domin matse/tsuke farji.  Idan mace tayi amfani da wani magani  gabanta ya tsuke/matse fiye da yanda maigidanta ya saba jinta zai iya sa maigidan yayi saurin kawowa saboda karuwar dadi ko dandanon jima'i.


5. Cututtuka masu shafar lafiyar jima'i, kamar cututtukan sanyin mara na maza da mata.


6. Ciwon damuwa ko fargaba na iya  haddasa saurin inzali. Misali, idan mutum yayi sabuwar amarya budurwa ko bazawara, idan yana fargabar ko zai iya gamsar da ita ko damuwa akan wani abu, wannan tunani zai iya sanya saurin inzali a cikin saduwar su.


7.  Yin istimina'i da gaggawa ( quick masturbation) da wasu matasa keyi kamin  su yi aure, musamman yara don gudun kada a kamasu (wasa da al'aura ko zinar hannu). Yana shafar lafiyarsu, yana haddasa saurin kawowa lokacin jima'i, sannan yana daga cikin alamomin raunin mazakuta. 



Related Posts:
Previous article
Next article

Leave Comments

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel