Menene alamomin Gonorrhea?
Menene alamomin Gonorrhea? |
Gonorrhea ciwo ne da ke shafar maza da mata da qwayar cutar Neisseria gonorrhoeae ke kawo shi.
Akan dauki ciwon da yada shi ta hanyar mu'amalar aure, ko daga uwa zuwa jariri. Ciwon kan shafi sassan jiki masu alaqa da mafitsara da haihuwa wato reproductive organs na duk maza da mata masu fama dashi.
Menene Alamomin Gonorrhea
Zuwa asibiti domin yin gwaje-gwaje da binciken da ya kamata ke tabbatar da ana dauke da Gonorrhea ko babu.
Amma akwai alamomin da sukan bayyana kamar haka :-
-Fitar da ruwa mai wari ko kalar qurji (pus)
-Jin zafi lokacin fitsari
-Painful ejaculation a maza
-Fitar da jini ko ba lokacin jinin Al'ada ba
-Kumburin Testis
-Ciwon mara mai tsanani
-Jinkiri ko rashin haihuwa
-Pelvic Inflammatory Disease a mata
-Ciwon maqogaro ko baki (Oral infection)da makamantansu ga masu oral sex
-Da sauran su
Rashin magance Gonorrhea kan iya haifar da matsalolin rashin haihuwa a maza da mata duka.
A bangaren mace akan samu yaduwar ciwon zuwa sauran gabobin jiki masu alaqa da haihuwa wato reproductive organs. Qwayoyin cutar kan haifar da abunda ake kira Pelvic Inflammatory Disease yadda hallitun wurin ba zasu iya gudanar da aiki yadda ya kamata ba, ko a samu tabo wato scarring a fallopian tube wurin da ke bada gudunmawa sosai wurin saukar qwan haihuwar mace da qyanqyashe shi idan ya hadu da qwan namiji.
A maza akan samu kumburin Epididymis wato wurin da yake taimakawa domin tafiya ko fitar da sperm lokacin ejaculation wanda hakan ke iya kawo matsalar rashin haihuwa a namiji.
Matakan Kare Kai Daga Gonorrhea
Hanya daya ce ta kare kai wato kamewa da daina mu'amalar aure barkatai.
Wadanda kuma hakan bai zame musu zabi ba to su ringa amfani da kwaroron roba (Condom) domin kare kai ko karsu yadawa wasu.
Amb(Nr)Sumayya Ibrahim Sa'ad
RN,RM,PND
Leave Comments
Post a Comment