Menene alamomin ciwon hanta (HEPATITISB) - Android Pols - latest news, natural remedies, and entertainment

Menene alamomin ciwon hanta (HEPATITISB)

Menene alamomin ciwon hanta (HEPATITISB)
Menene alamomin ciwon hanta (HEPATITISB) 


Ciwon hanta na daga cikin abinda ke damun mutane, hakan yasa wasu ke son sanin menene alamomin ciwon hanta da ya dace su sani domin magance matsalar. 


Alamomin ciwon hanta sun hada da;


  • Yawan zazzabi
  • Yawan kasala, da rashin jindadi ko kuzari ajika,
  • Rashin son cin abinci
  • Kaikayin jiki akai akai da yaki jin magani da dabaru, musamman in an wanka
  • Ganin koya mutum yadan quje fatarsa sai jini
  • Jin ciwon gefen ciki musamman bangaren dama daga kasan hakarkari, zuwa tsakiyar ciki. 
  • Yawan tashin zuciya koma ya zamto hade da amai lokaci-lokaci
  • Fitsari mai duhu ko kore-kore aga inya diga akaya baya fita yadda ya kamata da 
  • Kashi me kalar ruwan kasa-kasa
  • Ganin jijiyoyin jini wajen cibiya sun tashi sunyi rudu-rudu hade da kumburin ciki
  • Kumburin kafafu
  • Canzawar kalar idanu zuwa ruwan rawaya {yellow) 


Musamman daga sanda akaga idanu sun kaďa daidai wannan lokaci ne dole a dauki matakin kashe kwayoyin cutar domin kada su nakasar da hantar gaba-daya, wanda babban abin da suke kawowa shine Kurarraji ajikin hanta su sata ta motse ta lalacewa ta zamo yar karama. 


Daga nan cikin mutum zai fara tara ruwa ya soma kumbura kamar tanki abunda muke cewa ASCITES shikenan hakan yasa jini yakewa komawa da baya zuwa zuciya domin ba hanya wanda hakan zaisa zuciyar mutum ta sami matsala wato Heart failure wanda inba ai wani abu ba sai mutuwa. 


Ciwon hanta zafinsa ya bambanta daga jiki zuwa jiki. Kuma duk wanda ya kamu da Hepatitis B toh zai iya kamuwa da Hepatitis D. Domin ana ganin hepatits D ne kurum a mutanen da suke da Hepatitis B.... kunga kenan Double Trouble domin wadannan kwayoyi rukunin B na iya haddasa cutar kansar hanta wato Hepatocellular carcinoma... daka iya watsuwa ga sauran sassan jiki. Sabanin C da bata sa cancer saidai  anfi daukarta wajen karin jini amma kuma maimakon cancer ita ke lalata hantar ta sa mata kurarraji ta yadda za'a ga ciki ya kumbura dam... sannan mutum ya hadu da ciwon 


Menene Hatsarin Kamuwa Da Ciwon Hanta? ( Hepatitis B ) 


  • Mutane masu shan barasa/giya/burkutu 
  • Mutane masu ciwon sugar type2 
  • Mutanen masu yin zanen tattoos ajika, ko hujin kunnuwa, jiki da sauransuu 
  • Mutane masu kiba/te6a 
  • Mutanen dake shan magunguna daka, zarar sukaji wani ciwo ajika, walau na hausa ko turawa 
  • Amfani da sirinji guda daya wajen allura 
  • Amfani da Kayayyakin kaifi batare da kariya ba 
  • Masu jima'i batare da matakan kariya ba 
  • Mutane masu tarihin ciwon hanta cikin dangi 
  • Karin jini agida, ko kananun asibitocin daba kayan aiki ko doka bata yadda ba. 
  • Masu saida sinadaran chemicals na maganin kwari walau na noma . 


Allah yabamu lafiya Ameen


Related Posts:
Previous article
Next article

Leave Comments

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel