Menene ake nufi da yoyon fitsari?
![]() |
Menene ake nufi da yoyon fitsari? |
Vesico Vaginal Fistula (VVF)da a yaren hausa ake kira da yoyon fitsari na nufin samun buluwa ko hujewa tsakanin jakar ajiye fitsari (urinary bladder) da vagina a jikin mace.
Menene ake nufi da yoyon fitsari?
Yana faruwa bayan doguwar naquda da hakan kansa kan jariri ya danne mafitsara wadda suke makwabtaka da vagina ya hade su guri daya tare da jijiyoyin dake tare dasu. Haka zai sa su fara gugar wani bangare na qashin kwankwaso (friction), dalilin haka zai saka a samu qaranchi ko rashin zagayar jini a tare dasu (ischemia).
Dalilin haka wurin sai ya kumbura, naman wurin ya fara zagwanyewa sakamakon qaranchin jini sai a samu hujewa, hakan zai saka fitsarin dake cikin bladder ya fara samun hanyar shiga cikin vagina daga nan an samu yoyon fitsari.
MENENE DALILAN DA KE KAWO YOYON FITSARI?
Abubuwa da dama kan iya haifar da larurar yoyon fitsari musamman doguwar naquda ga mata masu qananun shekaru.
Sauran dalilan sune :-
-Doguwar naquda ko kuma Prolonged Labor da turanci .
-Idan aka samu wani abu ya rufe ko toshe hanyar da jariri zai fita daga mahaifa duk da yunqurin da uwa da jariri suke wurin ganin fitarsa ko kuma Obstructed labor da turanci.
-Criminal abortion :- Zubar da ciki bata hanyar da ya kamata ba.
-Unskilled delivery :- Rashin samun qwararrun masu karbar haihuwa.
-Trauma/Injury :- Gamuwa da larurar sakamakon hadari ko ciwo.
-Instrumental delivery :- Amfani da qarafuna yayin karbar haihuwa musamman ga wadanda ba qwararru ba.
-Chronic Pelvic Inflammatory Disease :- Idan qwayoyin cututtuka masu alaqa da mafitsara da haihuwa suka dade jikin mace ba tare da daukar matakin magance su ba
-Gynecological surgery/trauma :- Idan an taba yiwa mace tiyatar abunda ya shafi halittun cikin kwankwaso kuma aka samu akasi.
Anfi samun ciwon yoyon fitsari a wuraren da basu da qwararrun masu karbar haihuwa sannan da qaranchin wurin samun taimakon gaggawa da ya danganci haihuwa (Obstetric Emergency Services).
Amb(Nr)Sumayya Ibrahim Sa'ad
RN,RM,PND
Leave Comments
Post a Comment