Menene ake nufi da Mataccen Jini?
![]() |
Menene ake nufi da Mataccen Jini? |
Jajayen ƙwayoyin halittar jini suna da matsakaicin nisan kwanaki 120 suna zagayawa a cikin jijiyoyin jini. Daga nan kuma saifa da hanta su lamushe waɗannan tsofin jajayen ƙwayoyin halittar jini. A can kuma ɓargo ana cigaba da aikin ƙyanƙyashe sabbin jajayen ƙwayoyin halittar jini domin maye gurbin tsofi waɗanda saifa da hanta suke lamushewa da zarar kwanakinsu sun ƙare.
Haka Allah Ya shirya shiryayyen tsarin rayuwa da mutuwar ƙwayoyin jini a jikin ɗan'adam.
Saboda haka, macaccen jini ba ya zuwa wani sashin jiki ya taru. Sai dai, jini yana iya taruwa a wani sashin jiki idan aka samu bugu ko duka a sashin jikin.
Don haka, akwai buƙatar tantance dalilin yin ƙaho domin kauce wa yin ƙaho da hasashen cewa wai macaccen jini ne ya taru a sashin jikin.
© Physiotherapy Hausa
Leave Comments
Post a Comment