Menene ake nufi da Human Papillomavirus da abubuwan dake jawo shi?
![]() |
Menene ake nufi da Human Papillomavirus da abubuwan dake jawo shi? |
Human Papillomavirus rukunin qwayoyin hallitar virus ne da ke iya haddasa cutuka ga wanda suka shiga jikinsa ciki harda sankarar bakin mahaifa (Cervical Cancer).
Nau'in HPV din da kan iya haifar da larurar Sankarar bakin mahaifa ga mata na samun shiga jiki ne ta hanyar mu'amalar aure.
MENENE ALAMOMIN HUMAN PAPILLOMAVIRUS
HPV da kan iya haifar da larurar Sankarar bakin mahaifa ba'a iya ganeta da wasu alamomi domin bata nunawa, shiyasa yake da muhimmanci a yawaita zuwa asibiti domin yin gwaje-gwaje da binciken da ya kamata don ayi saurin gani ciwon Idan akwai.
Sauran rukunin HPV din kuma wasu sukan nuna alamomi ta hanyar bayyanar tsiro (warts) a sassan jiki kamar al'aura (Genital warts), fatar sauran jiki ko hannu da qafafuwa da sauran su. Zuwa asibiti domin yin gwaje-gwaje ke tabbatar da akwai ko babu a jikin mutum.
MUTANEN DA HUMAN PAPILLOMAVIRUS TAFI KAMAWA
-Masu qaranchin garkuwar jiki.
-Masu mu'amalar aure barkatai.
-Mata masu tura abubuwa (insertion) da sunan maganin mata.
-Masu budadden ciwon da baya samun kulawar da ta kamata da sauran su.
MATAKAN KARE KAI DAGA KAMUWA DA HUMAN PAPILLOMAVIRUS
-Yin allurar rigakafin HPV Vaccine
-Kamun kai da qauracewa mu'amalar aure barkatai.
-Mata su qauracewa saka abubuwa ko turawa a al'aurar su da sunan maganin mata.
-Cin abinchi mai gina jiki domin bunqasa garkuwar jiki.
-A ringa kula da ciwo Idan anji ta hanyar zuwa asibiti domin wankewa da allurar rigakafin sarke haqora.
-Da sauran su.
Amb(Nr)Sumayya Ibrahim Sa'ad
RN,RM,PND
Leave Comments
Post a Comment