Maza Masu Matsalar Ƙarancin Ruwan Maniyyi Ga Wani Haɗi Na Musamman Da Zai Taimake Ku — Android Pols

Maza Masu Matsalar Ƙarancin Ruwan Maniyyi Ga Wani Haɗi Na Musamman Da Zai Taimake Ku
Maza Masu Matsalar Ƙarancin Ruwan Maniyyi Ga Wani Haɗi Na Musamman Da Zai Taimake Ku


Barkanmu da wannan lokacin yaya ibada. Allah ya karɓi ibadun mu yasa mu dace da wannan wata mai alfarma na Ramadan. Yau insha Allah wata fa'ida ce nike tafe da ita ga mazaje masu ƙarancin ruwan maniyyi. Tun a baya dai mun sha yin bayani akan matsalar ƙarancin maniyyi wanda muka sha yin bayani akan sabubban da ke jawo hakan. Wasu halittace daga Allah.


Akwai kuma dalili na yin Istimna'i da kuma dalili na wato yin wasa da al'aura wanda muka sha yin bayani game da illolin da yake haifarwa masu yin sa ko mace ko namiji. Sai kuma dalilin yawan shan magungunan ƙarfin maza musamman na ƙwaya wanda suma suna taka rawar gani wajen haifar da ƙarancin ruwan maniyyi domin shan su yana ƙona maniyyi ga ɗa namiji.


Sai kuma matsala ta ciwon sanyi da sauran su. Wanda duk a shirye-shiryen mu na baya da suka gabata mun yi magana akan su. Kuma duk mun ba da taimako na yadda za'a magnace wannan matsala ta ƙarancin maniyyi, wanda mutane da dama sun jarraba kuma sun samu waraka. Shine a yau ma muka zo muku da wani sabon hanya da za ku yi maganin ƙarancin maniyyi.


Ka samu dabino mai kyau ba mai tsutsa bakamar guda 20 sai ka wanke shi ka cire ƙwallayen. Ka samu kofi mai kyau babba ka zuba dabino a ciki. Sannan sai ka samu ruwa mai kyau son samu ka samu ruwan roba domin yafi kyau idan kuma ba kada halin siya to ka samu ruwan leda sai ka zuba a cikin kofin da ka zuba dabino. Za ka barshi ya kwana. Da safe kafin kaci komai sai ka tsame dabino ka cinye, sannan kuma ka shanye ruwan.


Haka zaka ringa yi har tsawon wata 1, za kaga ikon Allah. In dai matsala ce akan ƙarancin ruwan maniyyi a sakamakon shan ƙwaya ko kuma wani abu makamancin haka to za ka samu waraka indai zaka ringa cin dabino ta hanyar da muka ambata. Wannan haɗin anyi shi kuma anga amfanin sa, kaima ka jarrab kagani. Allah ya sa mudace amin.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post