Maza Gareku, Yadda Ake Kula Da Mace A Zamantakewar Aure — Android Pols - Android Pols - latest news, natural remedies, and entertainment

Maza Gareku, Yadda Ake Kula Da Mace A Zamantakewar Aure — Android Pols

Maza Gareku, Yadda Ake Kula Da Mace A Zamantakewar Aure

 Yadda Ake Kula Da Mace A Zamantakewar Aure 


1 Idan tayi fushi jawota jikinka ka rarrasheta, mata suna son rarrashi. Hatta Manzon Allah SAW ya kasance yana rarrashin iyalinsa, kuma shi ne babban abin koyi ga kowa. 


2 Idan kaga tayi shiru tambayeta meye matsalarta cikin murya mai sanyi da tausasawa da tausayi da jin kai, ba wai da fada ba, al'adan mace ne ko anyi mata abu sai tace ba komai saboda ita komai sai tasa shagwaba kuma tana son mai rarrashinta. 


3 Idan tayi kwalliya ka yabawa kwalliya rta, idan tayi girki kaci kana santi koda dadinsa bai kai a yi santi ba. Domin idan baka yabawa za ta ga tayi kwalliyar a banza nan gaba baza ta kuma ba, ko kuma idan tayi ta dora a social media Nan zata samu masu yabawa. 


4 Idan kukayi kwanciyar aure da ita ka nuna mata kololuwar jindadinka da ita, haka kuma da rana ka dauko zance kana zuzuta ta kana yabawa da irin ni'imarta wannan shi zaisa ta kara kaimi wurin kula da kanta. Sannan ka fifita bukatar ta akan nata idan ka biya naka bukatar ka jira sai itama ta samu gamsuwa, inda baka da lafiya ka nemi magani idan baka iya ba ka koya. 


5 Kana yabon kyawawan halinta kuma kana tausa mata da yi mata uzuri idan tayi ba daidai ba.


6 Duk sanda ka samu lokaci kana shiga kitchen kana tayata ayyukan gida ko ba yawa ne, mata suna son su gansu tareda mazajensu suna tayasu aiki kai koda zuwa kawai kayi ka zauna bakayi komai ba za ta ji dadi a ranta.


7 Idan tace zata matsa daga kusa da kai riketa kace baka yarda ba, Idan kaga tana kuka sa bakinka ka tsotse hawayenta. Idan kaga tana kishinka kyaleta kar ka kyareta, so kesa ayi kishi wanda baya sonka ba zai yi kishinki ba. 


8 Idan bata da lafiya ka fita damuwa da halin da take ciki. Idan ka yi mata laifi ka nuna rashin jin dadinka da hakan kuma ka bata hakuri. 


9 Duk sanda zaka fita ka sumbace ta a goshinta. Kana kasuwa ko office kirata ta waya kace kana kewarta. 


10 Kada kalmar (ina sonki ta dinga yiwa harshenka nisa) Maza ku gane wani abu ba ci da sha da sutura ne kawai zakayi ka burge mace ba. Wata zakaga ba abinda ta rasa na nau'in jin dadi amma tana cike da damuwa me yasa? Saboda ta rasa abubuwanda na lissafo a sama. 


Wallahi akwai wanda sunfi shekara nawa suna samun matsala da iyalinsa sai kaji yana tutiyar bai rageta da ci ko sha ba sutura ma yanayi kawai halinta ne. Ba halinta bane ta rasa muhimman abubuwane a rayuwar ta. 


Sau da yawa anbar mazan hausawa a baya wurin kula da matansu kuma sune mafi dacewa da su kula da matansu idan mukayi duba da yanda Manzo S.A.W yakeyi da matansa. 


Allah ya bamu nagari Wanda zamu kula da dukkan hakkin su 


Related Posts:
Previous article
Next article

Leave Comments

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel