Matsaloli Biyar Da Ke Tilasta Dashen Gaɓar Ƙugu — Android Pols
Matsaloli Biyar Da Ke Tilasta Dashen Gaɓar Ƙugu |
Gaɓar ƙugu na daga cikin gaɓɓan da aka fi yi musu dashen gaɓa a cikin gaɓɓan jiki.
Gaɓar ƙugu ta haɗa da 'ƙwallon ƙashin cinya', wato kan ƙashin cinya da 'kwarmin ƙugu', wato ramin ƙugu da kan ƙashin cinya ke ciki.
Gabar ƙugu na lalacewa yayin da 'ƙwallon ƙashin cinya' da 'kwarmin ƙugu' suka sami karaya ko suka lalace sakamakon matsaloli kamar:
1. Karaya daga bugu, faɗuwa, faɗowa ko haɗuran ababen hawa.
2. Lalacewar ƙashi sakamakon ciwon sikila, wato amosanin jini.
3. Amosanin gaɓar ƙugu, wato matsanancin zaizayewar guruguntsin gaɓar ƙugu.
4. Lalacewar ƙashi sakamakon harɓin ƙwayoyin cuta a gaɓa, kamar tarin fuka (tarin TB) mai kama ƙashi, da dai sauransu.
5. Cutukan ƙashi kamar daji ko kansar ƙashi da sauran cutukan da ke zaizaye ƙashi.
Waɗannan matsaloli ne da ke lalata ƙashin gaɓar ƙugu kuma suna iya tilasta yin dashen gaɓar don ceto aikinta. Likitan tiyatar ƙashi ne ke jagorantar aikin dashen gaɓar.
Matsalolin da ke biyo bayan dashen gaɓar ƙugu sun haɗa da:
1. Ciwo daga gaɓar ƙugun zuwa ƙafa.
2. Kumburi.
3. Nauyin ƙafar.
4. Rauni/rashin ƙwarin tsokokin ƙafar.
5. Tabon yankan tiyata.
6. Riƙewar gaɓar ƙugu bayan dashe da sauransu.
Bayan likitan tiyatar ƙashi ya gama aikinsa, za a gayyaci likitan fisiyo don cigaba da kula da mara lafiyar domin shawo kan matsalolin da aka ambata har aikin gaɓar ya yi kyau, ƙafar ta yi ƙwari har mutum ya dawo tafiya ba tare da wata matsala ba.
Muhimman aikin likitan fisiyo a dashen gaɓar ƙugu sune: rage ciwo, rage kumburi, bunƙasa aikin gaɓar, bunƙasa ƙwarin tsokokin ƙafar, koya tafiya, da koya ayyukan yau da kullum ba tare da jin ciwo ko kuma lalacewar aikin ba.
© Physiotherapy Hausa
Leave Comments
Post a Comment