Matsalar Buɗewar Gaba Da Tusar Gaba |
Barkanmu da kasance a wannan lokacin yaya ibada, Allah ya karɓa mana amin. Maganar buɗewar gaba ko tusar gaba tare da abubuwan dake haddasa su. Duk macen dake fuskantar wannan matsalar yau nazo muku da wasu abubuwa da zaki haɗa su kina tafasawa kin zama a ciki na tsawon minti 20, to indai matsala ce akan tusar gaba da buɗewar sa to yazo ƙarshe.
Kamar yadda muka sha yin bayani a baya abubuwan da suke haddasa buɗewar gaban mace da jawo tusa suna da yawa, sai dai ba zamu samu damar ƙara yi muku bayanin su ba a wannan lokacin. Amma dai a taƙaice matsalar sanyi na daga cikin babban abinda ke jawo gaban mace ya buɗe wanda kuma hakan ke jawo ya ringa fitar da iska. Akwai matsalar rashin saka wando wannan na daga cikin abubuwan dake kawo shigar iska gaban mace kuma ba kowace iska ce zata shiga ba tare da ta ɗauko ƙura ba. Ita kuma ƙura akan iya samun ƙwayoyin cututtuka a tare da ita.
Akwai kuma matsala ta rashin tsaftace jiki da rashin yin wanka da wasu matan ke yi yakan jawo musu matsalolin sai ka samu wasu matan sun shafe kwana 3 ba suyi wanka ba. To idan ba'a yi wanka ba dole ne dauɗa ta taru a jiki idan kuma ta taru dole a samu ƙwayoyin cuta wanda sukan shiga cikin gaban mace su haifar mata da matsala. Rashin tsaftace wando shima yana daga cikin matsalar dake jawo tusar gaba, wasu matan sai su yi kwanaki 5 da wanda a jikin su ba tare da sun canja ba kuma ba su wanke ba.
Ana so a kullum ki sauya wanda kamar sau biyu idan kuma bakida damar yin hakan sai ki ringa wanke shi a kullum koda sau 1 ne hakan zai kare ki daga fuskantar shigar ƙwayoyin cututtuka cikin gabanki. Kuma banɗaki da kike amfani dashi ya zama koda yaushe a tsaftace duk da akwai matan da ba su kaɗai bane suke yin amfani da banɗaki ba na haɗaka ne. To ya zamana dai duk lokacin da zaki amfani dashi ki fara tsaftace shi ki wanke shi ki share dukkan wani datti dake wajen sai ki tsuguna kiyi amfani dashi.
Idan da hali ki daina yin kashi a masai irin ka gargajiya, domin irin wannan masan yana bada gudunmawa wajen haifar da shigar cuta cikin gaban mace. Akwai wani tiriri da yake tasowa daga cikin sa wanda idan mace ta tsuguna to zai shiga gabanta ne ya haifar mata da cuta. Don haka yi ƙoƙari ki bar yin amfani da irin wannan masan domin kiyaye kanki daga samun cutuka.
Idan kina fuskantar matsalar buɗewar gabanki da tusa ga wasu abubuwa da yakamata ki nema kamar haka;
(1) Bagaruwa
(2) Ƴayan hulba
(3) Garin Ganyen Magarya
(4) Miski
Idan kun tanadi waɗannan abubuwan sai ku tafasa su, sai a sauke daga kan wuta a samu ɗan gishiri a zuba kamar rabin ƙaramin cokali sai a juya a bar ruwan ya huce, ma'ana idan yai ɗumi sai ki zauna a ciki ruwan kiyi kamar minti 20 kina zaune a cikin sa. Za kiga irin ƙwayoyin cututtuka da za su fito daga gabanki. Idan kin wanke gabanki ki samu miski kaɗan ki goga shi a gaban naki. Kiyi hakan kamar na kwana 10 zaki rabu da tusar gaba kuma gabanki zai matse.