Matan Aure — Yadda Zaki Kare Kanki Daga Kamuwa Da Cutukan Sanyi

Matan Aure — Yadda Zaki Kare Kanki Daga Kamuwa Da Cutukan Sanyi
Matan Aure — Yadda Zaki Kare Kanki Daga Kamuwa Da Cutukan Sanyi 


Akwai matsala dake faruwa wanda ya shafi mata wanann matsala itace kusan ko ina suna fama da ita ta wato kamuwa da cutukan sanyi. Abinda zan yi bayani anan shine kodai kinsan cewa kina da wannan matsalar ko kuma baki da ita. 


Duk macen dake fama da matsalar na zo muku da hanya na yadda zaki kare Kanki daga kamuwa da cutukan sanyi. Wannan maganin da za ku yi amfani dashi domin ku magance kamuwa da cuta ko kuma ku yi rigafi daga kamuwa da cutukan sanyi.


Kuma shi wannan ciwo na sanyi ba wai iya manya ne ke kamuwa da shi ba, har da yara suma sukan kamu. Shiyasa idan za ki yi aiki da wannan maganin kiyi kokari ki hada da yaranki don kare su daga kamuwa da sanyi.


Shi wannan maganin tun daga mace 'yar shekara 3 zuwa 20 har ma da masu shekara 50 duk za su iya yin amfani dashi duk don kiyaye jiki daga samun wata matsala ta kamuwa da ciwon.


Kusan kowa akwai irin tasa matsalar musamman irin wannan matsala da mata ke yawan fuskanta ta kamuwa da ciwo, wanda ake kira da "toilet infection" wanda yawanci ake samun sa daga dubura. 


Idan za ku hada wannan maganin za ku samu garin lalle babban cokali 4  ku zuba ruwa kamar galan 1 wato lita 4. Sai ku hada ruwan da wannan garin lalle ku tafasa su. 


Ki samu roba mai fadi wacce za ki iya zama a ciki sai ki zauna a cikin wannan ruwan idan ya huce yadda ba zai kona ki ba. Zaki iya zuba gishiri kadan kamar rabin karamin cokali sannan ki zauna a cikin ruwan.


Idan kin zauna a cikin ruwan zaki yi kamar minti 30 a zaune a ciki sannan ki tashi, haka za ki dinga yi a duk bayan kwanaki uku Ko hudu. Suma yaranki haka zaki dinga yi musu suna zama a cikin ruwan, wannnan shine yadda zaki kare kanki daga kamuwa da cutukan sanyi.


Duk macen da za ta dinga yin wannan hadin tana zama a cikinsa to za ta rabu da kamuwa da ciwo kowane iri ne. Ko mace ba ta da ciwon idan tana yin wannan hadin zai zama kariya ne a gareta da kuma yaranta.


Sannan kuma duk mace mai matsalar kamuwa da ciwo wanda ke jawo mata kaikayin gaba, fitar farin ruwa mai kauri, warin al'aura da kuma fitowar kuraje a al'aura duk za ku iya yin amfani da wannan maganin. 


Duk wannan matsala za kiji tafita daga jikin ki, domin tun a lokacin da kike yin tsuguno za kiga wasu abubuwa da kike fitarwa na cuta daga al'aurar ki. Da fatan mata za ku yi amfani da wannan maganin.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post