MATAKAN KARE KAI DAGA KAMUWA DA LARURAR YOYON FITSARI — Android Pols
![]() |
YOYON FITSARI |
-Samar da wadatattu kuma qwararrun masu karbar haihuwa a cikin al'ummah.
-Samar da ingantattun kayan karbar haihuwa a asibitocin mu.
- A kiyaye a daina barin mata suna doguwar naquda musamman masu haihuwar gida.
-A guji yin ciki ta hanyar da bai kamata ba bare a yi qoqarin zubar dashi ta ko wacce hanya.
-A gujewa al'adar yankan gishiri ga yara mata (Female Genital Mutilation).
- A kula da tsaftar jiki, bayan gida da kuma yawaita wanke hannu kafin da kuma bayan shiga bandaki gudun kamuwa da Pelvic Inflammatory Disease.
-Aringa cin abinchi mai gina jiki yadda ko da ciwo ya kama mutum bazai masa illaba saboda akwai garkuwar jiki yadda ya kamata.
-Da sauran su
Ya kamata al'ummah su guji tsangwama da qyamatar masu fama da wannan ciwon saboda hakan na iya kawo musu ciwon damuwa (Depression).
Allah ya bawa masu fama da wannan ciwon lafiya, ya basu kudin iya kula da kansu da siyan magani. Ameen
Amb(Nr) Sumayya Ibrahim Sa'ad
RN,RM,PND
Leave Comments
Post a Comment