Mata Masu Matsalar Buɗewar Gaba Dalilin Ciwon Sanyi Ga Wani Haɗin Tsugune — Android Pols

Mata Masu Matsalar Buɗewar Gaba Dalilin Ciwon Sanyi Ga Wani Haɗin Tsugune
 Buɗewar Gaba 

 

Matsala akan sanyin gaba da tsagewar sa ko kuma ya dinga kwailewa ko kuma ya dinga daɗewa. To yawanci dai matsalar sanyi ce ta kan kawo hakan. Shiyasa irin wannan matsalar idan kina so ki magance ta to dole sai kin fara yin maganin sanyin dake cikin jikin ki sannan kuma sai ki haɗa maganin da zai miki maganin wannan matsalolin da muka ambata a farko.


Yawancin lokuta idan muka ba ku wata fa'ida ta magani musamman idan wanda ya shafi ciwon sanyi ne sai ku dinga cewa kunyi maganin kun samu waraka amma kuma bayan kwanaki kaɗan sai matsalar ta dawo. To abinda yake faruwa shine idan kunga hakan kuna da matsalar ciwon sanyi a cikin jikin ku wanda dole sai kun magance shi.


Don haka idan kuna so ku rabu da matsalar sanyi to dole dai kun ɗauki tsawon lokaci kuna shan maganin sa ba wai ku sha na kwanaki 5 ko sati 1 ko 2 ba. Sai kun ɗauki watanni kuna amfani da shi kafin ya gama bin jikin ku har ku samu waraka.


Mata Masu Matsalar Buɗewar Gaba Dalilin Ciwon Sanyi Ga Wani Haɗin Tsugune


Domin yin wannan haɗin na cutar sanyi zaki nemi abubuwa guda 3 domin ki haɗa wannan maganin.


(1) Garin Lalle, babban cokali ɗaya ko kuma ɗaya da rabi.

(2) Garin Magarya, shima kamar na farko kodai babban cokali ɗaya ko kuma ɗaya da rabi, duk yadda kukai ya wadatar.

(3) Kaninfari shi kuma kamar ƙaramin cokali ƙarami.


Zaki haɗa waɗannan abubuwan waje ɗaya ki zuba a cikin abinda kike yin girki ko tukunya ko wani abu makamancin sa. Sai ki zuba ruwa daidai misali Yadda ba zai yi yawa ba kuma ba ba zai yi kaɗan ba. Sai ki tafasa su su dafu sosai. Sai ki sauke daga kan wuta. Idan kin gama ba sai kin tace ba ki barshi hakan.


Sai ki ɗauko mai na miski ki ɗan zuba kaɗan a ciki, ki bari ruwan ya ɗan huce. Idan ya ɗan huce sai ki juye ruwan a baro mai faɗi wanda zaki iya zama a ciki sannan sai ki zauna a cikin wannan ruwan kiyi kamar minti 30 kina zaune. Idan kin tashi ki duba ruwan za ki ga abubuwan da zai wanke miki daga marar ki.


Kiyi haka duk bayan kwanaki 2 ko3 har na tsawon wata 2 kisha mamaki. Duk yadda kika kai ga matsalar ƙuraje, ƙaiƙayi, da daɗewar gaba. Insha Allah idan kinyi wannan zaki rabu da su. Amma ki tabbatar kin fara yin maganin sanyin cikin jikin ki shine idan kika yi wannan za kiji daɗin sa.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post