Masu Tambaya Kan: Menene Cryptocurrency?

Masu Tambaya Kan: Menene Cryptocurrency?
Menene Cryptocurrency?


"Yana da matukar muhimmanci idan kana crypto ka karanta wannan rubutun, sannan dan Allah kayi share dan wasu su ƙaru"


Tambayoyi sun yi yawa kan Menene Cryptocurrency? Amsa Anan shine: Ka ƙaddara a ranka crypto wani kuɗi ne na intanet, kamar dai yadda kuɗin takadda yake, sai dai kawai shi bambancin da kuɗin takadda shine shi a intanet yake. A maimakon kuɗin takadda da gwamnatin ƙasa ke da iko dashi, to shi cryptocurrency yana aiki ne akan wani tsarin intanet mai ƴanci wadda ake kira da "Blockchain".


Akan wannan tsarin intanet ɗin na Blockchain ake ajiye bayanan komai na kuɗin crypto, duk wanda ka turawa kuɗin crypto ko ya turo maka idan aka duba za'a ga wannan bayanan akan intanet na Blockchain. Tsarin intanet na Blockchain yana da tsananin tsaro fiye da normal intanet da muke dashi.


Bambancin tsarin Intanet na Blockchain da kuma Normal Intanet da muke amfani dashi shine: Misali kamar facebook yana kan normal intanet da muke amfani dashi, dan haka duk wanda yake amfani da facebook toh facebook suna da cikakken iko dashi. 


Toh da ace facebook akan tsarin intanet na Blockchain yake toh facebook basu da wani iko dakai. Wannan dalilin yasa ake wa tsarin intanet na Blockchain laƙabi da "Intanet Mai Ƴanci", kana da damar yin komai naka ba tare da tsangwama ba.


"Idan nace iko ina nufin: Facebook na da ikon rufe ma account naka, restriction dinsa, hana ka comments da sauransu. "


Toh su wannan kuɗin cryptocurrency ɗin akan tsarin intanet na Blockchain aka gina su, shiyasa suma ake musu laƙabi da "Kuɗi Masu Ƴanci". A maimakon yanzu idan kana da kuɗi a bankin ka, toh bankin nada iko dakai, toh su kuɗin crypto idan ka mallake su ka mallaka kenan ba wanda ya isa dasu idan ba kai ba.


Mai Tambayar: Tayaya ko Menene Yasa Kuɗin Cryptocurrency Suka Zama Kuɗi Da Har Kake Iya Chanza Su Ka Karɓi Naira?


AMSA: Kana ji yanzu idan na kirkiri kuɗin crypto akan Blockchain, da farko zan fara bashi adadi. Misali na kirkiri coin ɗin mai suna $ORC, dana tashi kirkirar sa sai na kirkiri guda 1Million. Toh da farkon lokaci dana kirkiri sa ba komai bane shi illa lambobi.


Lokacin da nake so ya zama kuɗi akwai hanyoyi guda 3 zuwa 5 da ake bi ya zama kuɗi, na 5 ɗin shine wanda yafi rikitarwa: (Menene Cryptocurrency) 


1. Na farko akwai abinda ake cewa ICO (Initial Coin Offering) ko kuma ace IPO (Initial Public Offering). Shi yadda tsarin yake shine: Zan dauki wannan coin ɗin nawa dana kirkira guda 1million mai suna $ORC, sai na bawa jama'ar gari dama akan su zo su sayi coin ɗin. Wannan kuɗin da za su yi amfani dashi gurin siyan coin ɗin, shine kuɗin da zai zama abinda ake kira Liquidity.


"Liquidity: kowanne kuɗin crypto na buƙatar shi, Liquidity shine yake baka damar idan kana da kuɗin crypto ka iya chanza shi a baka Dollar ko Naira. Toh wannan kuɗin da ake karba na ICO shi ake amfani dashi guri Liquidity". 


Mai Tambaya: Toh Dan Allah Kafin Ka Tafi Na 2, Ina Son Ka Faɗa Mini Su Waɗanda Suka Sayi Coin Ɗin A "ICO" Tayaya Suke Cin Riba, Ko Kawai Sakawa Suke Shikenan Kuɗinsu Ya Tafi A Wofi?


AMSA: Shi kuɗin crypto yana hawa da sauka ne, misali idan na sayi coin a ICO yana kan a ƙaddara ₦10, to yayin da ya shigo kasuwa mutane suka fara siye da siyarwa dashi. Farashin sa zai iya tashi ya zama ₦50, kaga kenan naci riba ko.


2. Bayan ICO, abu na biyu akwai abinda muke kira da IEO "Initial Exchange Offering", shima dai kamar ICO yake. Sai dai shi a maimakon zuwa da zakayi ka sayi coin direct ta hannun masu coin ɗin, shi IEO a kasuwannin crypto akeyin sa irin su Binance, Kucoin, CoinEx, Bitget da sauransu.


3. Akwai kuma IDO "Initial Dex Offering". 

"A crypto akwai tsarin gurin siyayya guda biyu, na farko akwai CEX "Centralized Exchanges" su gurin siyayya ne na crypto da suke aiki kamar banki, sai kayi KYC kayi komai kafin ka fara amfani dasu. Akwai kuma DEX "Decentralized Exchanges" asalin tsarin crypto kenan, shi kuma ba abinda ake buƙata kawai budewa zakayi ka fara amfani dasu"


Toh IDO anayin sa ne a gurin musayar crypto na DEX, shima duk yana aiki ne irin yadda ICO da IEO suke.


4. Sai kuma IFO "Initial Farming Offering", shi kuma sani tsari ne da akeyi wanda za'a ce ka sayi wani coin da tuntuni yana kasuwar crypto ka ajiye sa, za'a dinga baka wannan sabon coin ɗin da bai shigo kasuwa ba kyauta.


5. Sai na ƙarshe wanda yafi kowanne ruɗarwa shine IAO "Initial Airdrop Offering". Shi kuma coin ɗin ake rabawa kyauta ga mutane, amma fa dabara ce da ake amfani da ita dan tara mutane. Misalin irin wannan tsarin, akwai mining da mukeyi.


Suna dabara su tara mutane ta hanyar alkawarin zasu basu coin ɗin su kyauta, sai su ce musu suyi wani aiki. Lokacin da wa'adi ya cika, dama a chan gefe guda akwai wasu manya masu kuɗin crypto da kasuwanni da zasu ga.  Ai project kaza yana da mutane da yawa.


Don haka sai su dauki kudinsu su saka a matsayin Liquidity a sa coin ɗin a kasuwa, su kuma sai a basu wani adadi na coin ɗin, misali coin ɗin guda miliyan daya ne, sai a basu dubu 500k. Sai ace to a hankula zuwa wani lokaci zasu siyar da coin ɗin da aka basu.


Mai Tambaya: Toh Su Ta Taya Ake Suke Mayar Da Wannan Mahaukatan Kuɗaɗen Da Suke Sakawa Ake Baiwa Mutanen free...?


AMSA: Na faɗa muku cewa kuɗin crypto hawa yake da sauka ko? Toh mutane sune suke zama sanadin hawan nan nashi da sauka, yayin da suka dinga siya toh farashi zai tashi yayin da sukayi ta siyarwa toh farashi zai sauka.


Toh karka manta coin ɗin da akayi mining dole yana da mutane bila'adadin da suka san shi, dan haka akwai mutanen da muke kira da Traders da kuma Holders a crypto. Da zarar sun samu labarin coin ɗin zasu fara saka kuɗi, hakan zai sa ya dinga tashi.


Ta yiwu an saka shi a ₦100 duk guda daya, toh bayan Traders da Holders sun fara siya sai kaji farashin ya dawo ₦800. Su kuma wannan manyan masu kuɗin crypto da kasuwannin dama an basu guda dubu 500k, kamar yadda aka musu alkawari.


Sune suka saka masa kuɗi ya fito a farashin ₦100, kaga kenan idan suka siya a ₦100, sai dai ma su faɗi basu ci riba ba. Amma da sun tsaya yaje farashin ₦800, toh yanzu ya ninka musu kuɗin su x7. Kaga suna cikin riba.


Akwai coins da yawa a kasuwar crypto, yanzu haka akwai guda sama da dubu 30k. Dan haka babban abinda kowanne project na crypto suke nema shine a sansu, ba kuma za'a san su ba sai mutane sun san su. Hakane yasa suke neman mutane suyi mining ko task.


Yin wannan mining ɗin da task ne yake sawa duniyar crypto ta san project din, tunda maybe dubbunai ko miliyoyin mutane ke mining ɗin ko task. Dan haka da zarar ya fito, Traders da Holders na crypto suke fara siyansa. Wannan ke sawa farashin sa ya tashi. 


Wannnan dai shine bayani kan menene cryptocurrency, wanda mutane da dama ke yin tambaya a kullum. Da fatan duk wanda ya karanta ya ƙaru kuma ya amfana. Nan gaba za mu ƙara faɗaɗa bayani kan cryptocurrency. Allah yasa mudace amin. 


#Imamu_Sheka

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post