Maganin Zazzaɓin Cizon Sauro — Android Pols - Android Pols - latest news, natural remedies, and entertainment

Maganin Zazzaɓin Cizon Sauro — Android Pols

Maganin Zazzaɓin Cizon Sauro
Maganin Zazzaɓin Cizon Sauro 


Masatalar cizon sauro mastala ce da ta addabi kusan kowa da kowa domin kusan duk gida akwai wannan matsalar musamman a wannan lokacin na zafi. Cizon sauro ya kan haifar da zazzabi mai zafi a jikin mutum. A wasu ƙasashen idan mutum ya kamu da zazzaɓin cizon sauro akan killace shi domin bashi agaji har sai ya warke.


Abubuwa da yawa suna jawo sauro zuwa wajen da kuke a sakamakon yin mu'amala da ruwa, wajen ajiye kayayyaki ba tare da kula dasu da kuma tsaftace wajen ba. Sannan wajen da muke ajiye shara wanda wasu masana ke cewa tarin shara yana daga cikin babban abinda ke jawo sauro. Wasu mutanen ma a cikin ɗakin su suke tara shara kaga kuwa dole sauro yazo ya zauna.


Idan kuna son ku rage yawaitar sauro dole sai kun ɗauki wasu matakai na kariya a gidajen ku da kuma inda kuke rayuwa. Ku tabbatar kun daina tara shara a wajen da kuke zaune kodai a cikin gida ko ɗaki ko bayan gida, ku tabbatar duk lokacin da kuka tara shara kun ɗebe kun zubar da ita. Sannan kuma ku tabbatar da kuna kwashe kwata a gidajen ku domin kwata na ɗaya daga cikin abubuwan da ke jawo sauro.


Sai dai wasu na ƙorafin cewa duk da gyaran da suke yi da tsaftace muhallin su amma hakan bai hana yi musu maganin Cizon sauro ba wanda ke iya haifar musu da zazzaɓi. Shiyasa a yau muka kawo muku wani magani na zazzaɓi cizon sauro da za kuyi amfani dashi domin samun sauƙi, kuma idan kuna sha za ku kare kan ku daga kamuwa da wannan zazzaɓin na sauro.


Maganin Zazzaɓin Cizon Sauro 


Ga abinda za ku nema domin ku haɗa wannan maganin na zazzaɓin cizon sauro, za ku samu ganyen gwaiba da kuma ruwa sannan zuma, amma ita zuma ba dole bane. Wannan sune kaɗai abubuwan da ake buƙata. Shi ganyen na gwaiba guda 2 kacal za ku samu sai kuma ruwa kamar kofi ɗaya babba wato lita 1 kenan. Sai ku zuba a tukunya ku tafasa su.


Idan ya tafasa sai ku sauke ku barshi ya ɗan huce. Za ku ringa ɗiban wannan ruwan a ƙaramin kofi kuna sha da safe da rana da kuma dare. Idan kuma kuna da halin siyan zuma duk lokacin da zaku sha sai ku zuba kamar cokali 1 idan kuma babu hali shikenan sai kusa haka. Indai matsala ce akan zazzaɓin cizon sauro duk gidan da suka riƙe wannan maganin to za ku rabu da wannan zazzaɓin.


Amma idan zazzaɓin ba iya na cizon sauro bane akwai na taifod to za ku samu ganyen gwanda kamar guda 2 sai kuma ganyen gwaiba guda 5 ku haɗa su ku zuba ruwa babban kofi 2 wato kamar lita 4 sai ku dafa. Idan ya tafasa sai a zuba shi a wajen da ba zai lalace ba. Shima za ku ringa sha a kullum kamar sau 3. Shima kamar wancen zaku iya haɗawa da zuma ku sha.


Related Posts:
Previous article
Next article

Leave Comments

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel