Maganin Ulcer |
Ga wata falala da wani bawan Allah yace a sanar daku kuma idan kunji ku sanar da bayin Allah su ma su yi. Gyambon Ciki wanda a turance ake kira da 'ULCER' yace kowace iri ce insha Allah idan aka sha wannan maganin zaka rabu da ita. Akwai waɗanda suke yin shaƙuwa, mai yawan yin gyatsa mai sa mutum ya ringa yin kumallo ko kuma mai sa ciwon baya da riƙewar kafa da kuma wacce take jawo zazzaɓi da ciwon kai.
Kai duk wani abu da yake da dangantaka da ciwon ciki in Allah ya yarda zaka rabu dashi. Ba wai sauƙi zakaji na ƴan kwanaki ba zaka rabu da ciwon gabaki ɗayan sa. Idan kun karanta wannan rubutun to kuyi ƙoƙarin yin amfani da abinda muka faɗa, idan kuwa kasan ko kinsan bakida buƙata to nasan a gidanku ba zaku rasa masu wannan ciwon na gyambon ciki ba domin ta zama gidan kowa akwai.
Maganin Ulcer Ko Wane Iri Ne Duk Tsananin Ta
Zaku nemi ayaba manya guda 4 waɗanda ake kira da plantain da yaren turanci, idan kuma ba'a samu manyan ba sai a samu madaidaita kamar 5. Sannan kuma waɗanda ake da buƙata ba wanda suka nuna ba. Zaku ga jikin su kore babu nuna ajikin su to su zaku nema. Idan kun same su sai ku ɓare bawon su ku yayyanka su. Sai ku samu jarka irin mai lita 4 ku zuba ayabar a ciki.
Idan kun zuba a cikin jarkar sai ku zuba ruwa a ciki ku rufe da murfi, zaku barshi yai kwana 3 sai ku ɗauko jarkar ku girgiza sannan sai ku ɗauko kofi ku tace daidai iya wanda zaku iya sha a lokacin. Amma da safe zaka sha kafin aci abinci. Idan kunci abinci bayan kamar minti 30 sai ku ƙara zubawa a kofi ku sha. Sannan kuma da rana idan kinci abinci sai ki ƙara zuba rabin kofi kisha.
Ba zaki ƙara sha ba sai da dare idan anci abinci sai a sha. Haka zaka kuma yi gobe. Idan ruwan ya ƙare sai a zubar da diddigar. Sannan kuma a sake samo plantain ɗin guda 4 kamar yadda kuka yi na farko ku ƙara zubawa a jarkar ku zuba ruwa yai kwana 3 a ajiye, sai dai za kuji babu daɗin sha amma dai haka ake yin sa. Kuma haka zaku ringa yi kamar sau 4 domin zai yi muku maganin ulcer.
Yace indai anyi kamar sau 3 ko 4 to angama da matsalar ulcer ko wace iri ce ko takai chronic za'a rabu da ita gabaki ɗaya. Indai zaka daure ka sha jarka 3 to babu shakka zaka rabu da gyambon ciki gabaki ɗaya. Don haka kuyi ƙoƙari ku jarraba kuma za'a samu nasara da yardar Allah. Don girman Allah ku sanarwa da al'umma wannan sirrin.