Lafiya
Maganin Ciwon wuya — Android Pols
Wednesday, January 29, 2025
0
Maganin Ciwon wuya |
Maganin CiwonWuya, Akwai gungun tsokoki a wuya da yawa. Wasu suna waiwaye dama zuwa hagu ne, wasu suna sunkuyar da kai, wasu kuma suna ɗaga kai ne.
Har wa yau, ya kamata a tuna cewa wuya yana ƙunshe da muhimman abubuwa kamar laka, jijiyoyin laka, jijiyoyin jini, ƙasusuwa, tsokoki da sauransu.
Ciwon wuya ko riƙewar wuya na iya kasancewa daga matsalar gaɓoɓin ƙasusuwan wuya, jijiyoyin lakar wuya, ko kuma tsokokin wuya.
Kiyayi miƙa wuyanka ga wanda ba ƙwararre ba da sunan "gyara" saboda ciwo ko riƙewar wuya.
Miƙa wuya ga wanda ba ƙwararre ba tamkar miƙa wuya ga haɗari ne!
Ciwon wuya ko riƙewar wuya na buƙatar ganin likitan fisiyo domin magance matsalar daga tushe ba tare da shan ƙwayar magani kullum ba.
© Physiotherapy Hausa
Previous article
Next article
Leave Comments
Post a Comment