Maganin Ƙaiƙayi Da Fitowar Ƙuraje A Fuska Bayan Aski |
Akwai waɗanda idan sunyi aski suke jin ƙaiƙayi ko kuma fesowar ƙuraje, musamman wasu mazan idan sun aske gemu a haɓarsu sai ƙaiƙayi ko kuma bayan ƙeya shima idan anyi gyaran fuska yakan jawo ƙaiƙayi. Ko kuma wasu idan sun aske gashin hammatar su shima yakan jawo ƙaiƙayi. Wasu kuma gashin marar su idan sun aske yakan jawo su yi ta jin ƙaiƙayi.
To ga dukkan wanda yake jin hakan ga maganin ƙaiƙayi idan yayi aski ko kuma yake ganin wasu ƙuraje suna fito masa. To ga wasu abubuwa guda 2 da zaku yi amfani dasu ta hanyar shafawa kafin kuyi askin. Kamar yadda zaku shafa sabulu a jikin ku idan za kuyi wanka shima wannan abin da zaku yi amfani dashi haka zakuyi. Idan gashin hammata zaku aske sai ku kwaɓa ku shafa a gashin sannan sai ku aske.
Maganin Ƙaiƙayi Da Fitowar Ƙuraje A Fuska Bayan Aski |
Idan gashin mara ne shima haka zaku shafa haka idan gyaran fuska ne shima haka za kuyi. Idan zaku ringa yin hakan kuna shafawa a duk lokacin da za kuyi aski to indai maganar ƙaiƙayi ne ko kuma fitowar ƙuraje za kudaina ganin su. Zaku samu farin man goge baki akwai kanfanoni iri-iri sai ku samu mafi inganci. Sai kuma ku samu lemon tsami ƙarami ku raba shi gida biyu ku ɗauki rabin ku maste ruwan.
Sai ku hada ruwan lemon tsamin da wannan farin man na goge baki sai ku cakuɗa, idan za kuyi gyaran fuska sai ku shafa akan gashin idan kuma askin mara zakuyi shima sai ku shafa ko kuma idan na hammata zaku yi shima sai ku shafe hammata dashi. Idan kun shafa sai ku aske to ba za kujiwani ƙaiƙayi ba. Sannan kuma ba zaka ga wasu ƙuraje sun fito maka ba.
Kada kuyi wasa da wannan haɗin domin yana yin aiki sosai. Kuma mutane da dama sun yi amfani dashi ya yi musu aiki. Don haka kaima ko kema idan kina fuskantar irin wannan matsala ta jin ƙaiƙayi idan kinyi aski ko idan kayi gayran fuska kana ganin ƙuraje suna fito maka to yi gaggawar yin amfani da waɗannan sinadaran da muka ambata domin samun waraka.
Idan kunyi kunji daɗin sa kuyi ƙoƙarin sanarwar da sauran jama'a domin akwai waɗanda suke da irin wannan matsalar amma kuma ba su san hanyar da za su bi domin su samu magani ba. Amma idan kun sanar dasu zasu samu suyi kuma ku da kuka sanar musu zaku samu lada.