LABARIN WATA MATA DA TA ƊANƊANA ABINCIN ALJANNA A MAFARKI
LABARIN WATA MATA DA TA ƊANƊANA ABINCIN ALJANNA A MAFARKI |
Al-Imam Hakim (Allah ya gafarta masa) ya kawo wani labari mai ban mamaki a littafinsa mai suna (تاريخ نيسابور).
Wata mata ce mai suna Rahama Bint Ibrahim wacce ke zaune a wani gari mai suna Hazorasp (Yanzu garin yana ƙasar Uzbekistan ne) ta kasance ba ta cin abinci ko abin sha; ta rayu a haka fiye da shekaru 20!
Ya abin ya faru?
Mijin wannan baiwar Allah ya kasance an kashe shi ne a wajen wani jihadin kare garinsu lokacin da aka kawo musu hari. Ya mutu ya bar ta da yara guda biyu. Ya kuma bar su cikin halin talauci da rashi.
Wata rana ta idar da sallar Magriba sai ta zauna tana addu'a, ba ta ankara ba, sai barci ya kwashe ta. Sai ta yi mafarki ta gan ta a wani waje cike da mutanen da aka karkashe tare da mijinta. Suna ta biki suna shagali da sharholiyarsu. Sai ta tambayi wani cewa don Allah ina mijina? Sai ya ce mata: bi nan wajen za ki gan shi. Ta ce: ina zuwa can gaba sai na gan shi tare da wasu abokansa waɗanda aka kashe su tare suna zaune gaban wani babban teburin cin abinci.
Ko da ya ganni sai ya ce da abokansa, don Allah in ba za ku damu ba, wannan miskiniyar tun jiya ba ta ci komai ba. Ku bari na ɗan sam mata wani abu mana ta ɗan taɓa. Sai suka ce ba komai, ka ba ta. Sai ya miƙo min wani ɓantaren gurasa fara sal kamar nono ga daɗi kiye da dadin sukari ko na zuma, sannan kuma laushin gurasar kamar laushin man shanu.
Sai ta ce: Da na sanya a bakina na tauna na haɗiye, sai ya ce min tashi ki tafi, daga yau ba ke ba jin yunwa har ki bar duniya. Daga nan sai ta farka firgigit.
Daga nan ba ta ƙara jin yunwa ba. Ba ta ci ba ta sha ba ta tsuguno. Sannan kuma ba ta son jin ƙamshin abincin duniya. Takan ce wari yake yi, in ana cin abinci a kusa da ita sai tana toshe hancinta.
Al-Imam Az-Zahaby (Rahmatul Lah Alaihi) da ya kawo labarin nan a (Siyar) ɗinsa sai ya ce: "wannan labari ne tabbatacce." Tsarki ya tabbata ga Allah wanda ke da iko akan komai.
Dr Kabir Asgar
Leave Comments
Post a Comment