Kofar Da Shiga Ba Dawowa (The Door of No Return) - Android Pols - latest news, natural remedies, and entertainment

Kofar Da Shiga Ba Dawowa (The Door of No Return)

Kofar Da Shiga Ba Dawowa (The Door of No Return)
Kofar Da Shiga Ba Dawowa (The Door of No Return) 


Me ake nufi da Ƙofar Ba Komawa?


Gidan da ke kallon Tekun Atlantika, tsohon wurin cinikin bayi ne, gida ne ga abin da ake kira "Kofar Ba Komawa," inda aka tilasta wa miliyoyin 'yan Afirka shiga jiragen ruwa na bayi da ke zuwa Amurka.


Kofar da idan aka fice ta cikinta ba a dawowa (The door of no return). Wannan wata kofa ce wacce idan mutum ya fice ta ciki bazai taba dawowa ba ya tafi kenan har abada (The door of no return) sunanta.


Kofar tana kasar Senegal a tibirin goree, mafiya yawan yan Africa sunbi ta cikin wannan kofar hannu da kafarsu daure da sasari inda turawa suka dauke su a matsayin bayi shekaru 400 da suka wuce. Duk lokacinda ka fice ta cikin kofar nan to shikenan kayi bankwana da yan uwanku da sauran danginku.


Gaba daya rayuwar mutum ta baci ya zama bawa kenan a gurin turawa, domin ta wannan kofar sukai ta ficewa da mutanen da suka kama a matsayin bayi a wancan lokacin.


Tsibirin Gorée, mai nisan kilomita biyu daga tashar jiragen ruwa ta Dakar, na cikin wuraren da hukumar ilimi da al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya ta ayyana a matsayin wuraren tarihi na duniya. Kuma daya ne daga cikin wurare na farko da Turawa suka zauna a nahiyar Afirka. Tsibirin ya samo sunansa ne daga tsibirin Goeree na kasar Holland; kasasncewar Turawan Holland din sun mamaye tsibirin a shekarar 1588. Kafin nan, turawan kasar Portugal sun zauna a tsibirin a shekarar 1444. Da akwai hoton da ke nuna yadda ake iya hango tsibirin Gorée daga karamin jirgin ruwan da ke tasowa daga tashar jiragen ruwa ta Dakar.


Gidan Bayi" na tsibirin Gorée, ko "Maison des Esclaves" a Faransanci, na cikin wuraren tarihi da suka sanya tsibirin Gorée ya shahara. 'Yan yawon bude ido da dama ne dai ke kai ziyara tsibirin, musamman ma gidan, don ganin abubuwan tarihi na bauta, ko da yake wadansu manazarta suna tababa a kan yawan bayin da aka dauka daga tsibirin zuwa nahiyoyin Turai da Amurka. A kwai hoton da ke nuna kofar shiga Gidan na Bayi, kuma a cewar shugabansa na farko tun bayan mayar da wurin gidan adana kayan tairihi. Bayi fiye da miliyan daya sun wuce ta gidan.


Kofar Karshe: Daga wannan kofa da ake gani a wannan hoto, wacce ke kuryar Gidan Bayi, ba dawowa. Daga bakin ruwa ake diban bayin a kwale-kwale a kai su manyan jiragen ruwan da ke can cikin teku. Wanda yayi kokarin gudu ta hanyar fadawa teku, mutuwa zai yi, wanda kuma ya ki shiga jirgi harbe shi ake yi. Sai dai kuma masana tarihi sun yi sabani a kan ko don cinikin bayi zalla Turawa suka yi amfani da Tsibirin Gorée, ko kuma cinikin bayin na wani dan karamin bangare ne na kayan da aka yi safara zuwa Turai da Amurka.


Rubutun farko na cinikin bayi a can ya samo asali ne tun 1536 kuma mutanen Portuguese ne suka gudanar da shi, Turawa na farko da suka taka Æ™afa a tsibirin a shekara ta 1444. An gina gidan bayi a shekara ta 1776. mutanen Holland ne suka gina shi, shi ne gidan bayi na Æ™arshe har yanzu  yana nan a Goree kuma yanzu yana aiki a matsayin gidan kayan gargajiya. Ana É—aukar tsibirin a matsayin abin tunawa ga Black Diaspora.


Kimanin 'yan Afirka miliyan 20 ne suka ratsa tsibirin tsakanin tsakiyar 1500s zuwa tsakiyar 1800s. A lokacin cinikin bayi na Afirka, tsibirin Goree ya kasance wurin ajiyar bayi, cikakkiyar cibiya ce ta kasuwanci a tsakanin maza da mata da yara na Afirka. An kama miliyoyin 'yan Afirka ta Yamma ba tare da son ransu ba. An kawo wannan Waje, ' tsibirin Goree, an sayar da su a matsayin bayi, kuma an ajiye su a cikin ajiyar da ke tsibirin har sai an yi jigilar su zuwa tekun Atlantika. An sayar da su a Kudancin Amurka, Caribbean, da Arewacin Amurka don ƙirƙirar sabuwar duniya. Yanayin rayuwar bayi a tsibirin Goree ta kasance cikin mummunan hali.


Lokacin da Faransawa ta soke bauta a cikin 1848, mutane 6000, 5000 daga cikinsu tsoffin fursuna suna zaune a tsibirin.


Hukumar UNESCO ta Majalisar Dinkin Duniya ta kebe tsibirin don zama Gidan Tarihi na Duniya, Tsibirin Goree a karni na 21 ya rike tare da adana duk abubuwan da suka faru a baya.


Related Posts:
Previous article
Next article

Leave Comments

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel