Ko kunsan Shan Agwaluma Na Tataimakawa Wajen Maganin Cutuka A Jikin Ɗan Adam — Android Pols

Ko kunsan Shan Agwaluma Na Tataimakawa Wajen Maganin Cutuka A Jikin Ɗan Adam — Android Pols
 Maganin Cutuka da Agwaluma ke yi A Jikin Ɗan Adam 


Kamar yadda muka sha yin bayani cewa magunguna sunanan babu adadi, ƴaƴan itatuwa da muke yin amfani dasu da wanda muke cin ƴaƴan su da waɗanda muke amfani da jijiyoyin su da waɗanda muke amfani da ganyen su kowane yana da irin tasa fa'ida tare da bayar da gudummawa ga jikin ɗan Adam, sai dai kawai abinda mutum ya sani.


Shan Agwaluma Na Tataimakawa Wajen Maganin Cutuka A Jikin Ɗan Adam


kullum bincike ake yi akan abinda ya shafi maganin gargajiya domin taimakawa al'umma domin samun lafiyar jikin ɗan Adam. Akwai abubuwan da abinci ne amma kuma magani ne suna nan babu adadi. Bincike ya gano amfani da maganin da ake samu daga shan Agwaluma ga jikin Ɗan Adam.


Ita dai Agwaluma nau'i ce na kayan itatuwa wacce yawancin masu yin amfani da ita ba su san cewa tana yin wani magani ba suna sha ne kawai domin sha'awa ko kuma wanke baki. Wannan Agwaluma da ake ɓareta akwai wacce zaka ji tana da tsami wata kuma da zaki. To ita dai Agwaluma tana da amfani matuƙa dagaske a jikin ɗan adam. Shiyasa a yau muka kawo muku wasu daga cikin maganin da take yi a jikin ɗan adam da bakowa ya sani ba.


Ita Agwaluma tana ɗauke ne da sinadarin bitamin C wanda yake bada gudunmawa wajen yaƙi da cutuka da dama a jikin ɗan adam. Ga wasu kaɗan daga cikin maganin da ita Agwaluma keyi ga jikin dukkan wanda ke amfani da ita kamar haka;


(1) Idan mutum baya son ya dinga yin ƙiba ko mace ko namiji, ma'ana idan mutum bayaso kitse yaimasa yawa a jikin sa to ya ringa shan Agwaluma zai kiyaye kansa da girman jiki da ƙarin kitse.


(2) Masu fama da rashin barci ba tare da wani dalili ba, haka kawai mutum yaji ya kasa yin barci to ku ringa shan Agwaluma za ta taimaka muku wajen samun barci a duk lokacin da kuke son ku yi. Indai mutum zai ke shan guda 1 a rana to duk wani abu dake hana ku barci to za'a samu waraka.


(3) Shan Agwaluma yana taimakawa wajen maganin rage ciwon ciki. Duk wanda ke fama da ciwon ciki to idan yana yawan shan Agwaluma za ta taimaka masa wajen magance matsalar da ke haddasa ciwon cikin.


Wannan sune kaɗan daga cikin jerin abubuwan da Agwaluma ke maganin su idan mutum yana yawan amfani da ita. Ga dukkan wanda ke fama da matsala ta rashin samun barci ko kuma ciwon ciki ko kuma waɗanda ba su son su yi ƙiba to muna fatan za ku gwada shan Agwaluma domin za ta taimaka muku. 


Nan gaba za mu kawo muku ƙarin wasu daga cikin ayyukan da Agwaluma keyi ga jikin ɗan adam.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post