Kanal Victor Banjo Soja Bayarbe Da Yayi Yaki A Karkashin Tutar Biyafara
![]() |
Kanal Victor Banjo Soja Bayarbe Da Yayi Yaki A Karkashin Tutar Biyafara |
Victor Banjo An Haifeshi a ranar 1 ga watan Afrilu 1930 ya mutu a ranar 22 ga watan Satumba 1967. Ya kasance Kanar a rundunar sojojin Najeriya. Amma daga baya ya koma cikin sojojin kasar Biyafara a lokacin yakin basasar Najeriya. An yi kuskure wajen sanya sunan Victor Banjo a cikin wadanda suka shirya juyin mulkin ranar 15 ga watan Janairu 1966 juyin mulkin da ya kawo gwamnatin Aguiyi Ironsi.
Sai dai a lokacin da yake yaki tare da sojojin Biyafara an zarge shi da yunkurin yiwa Ojukwu juyin mulki kuma an kashe shi a sakamakon haka. Alkalin kotun soja ta biyu ne ya yankewa Victor Banjo hukunci, domin alkalin kotu ta farko ya bayyana cewa babu isassun shaidun da za su iya yankewa Victor Banjo laifin juyin mulki. Kawo yanzu dai babu wani bangare da ya tabbatar da hannun Victor Banjo a juyin mulkin guda biyu a Najeriya ko a kasar Biyafara. Zarginsa da hannu da akayi a duk wani yunkurin juyin mulki ya zama jita-jitar da ba ta da tushe.
Laftanar Kanar Victor Adebukunola Banjo, shi ne Darakta a bangaren injiya na Farko na Hukumar Lantarki ta Sojojin Najeriya. Ya shiga aikin Soja a shekarar 1953 a matsayin Warrant Officer 52 kuma shi ne dan Najeriya na sha shida da aka ba mukamin hafsa. (NA 16). Wanda ya halarci Kwalejin Soja ta Royal Sandhurst dake kasar ingila, ya kuma sami B Sc. a Injiniya.
Hankalin Banjo ya fara tashi ne bayan juyin mulkin ranar 15 ga Janairu, 1966, wanda ya kawo Manjo-Janar Thomas Johnson Aguiyi-Ironsi kan karagar mulki.
Kwanaki uku da hawan Aguiyi-Ironsi kan karagar mulki, an gayyaci Banjo zuwa ofishin babban kwamandan soji, aka kama shi a lokacin da yake jiran ganin shugaban kasa. An zarge shi da yunkurin kashe Shugaban kasa kuma aka tsare shi. A wasu rubuce-rubuce a wancan lokaci mai cike da tashin hankali a tarihin Najeriya ance an tsare Banjo ne saboda ana tunanin yana da hannu a juyin mulkin ranar 15 ga Janairun 1966. Wannan lokaci ne mai wahala ga Najeriya domin juyin mulkin ranar 15 ga watan Janairu ya rura wutar kabilanci da kuma raba kan sojoji, kuma Aguiyi-Ironsi ko kadan bai san yadda zaiyi ya shawo kan matsalar ba.
An tsare Banjo a gidajen yari daban-daban tsakanin watan Janairu 1966 zuwa Mayu 1967. Banjo Yana da mace tare da ’ya’yansu huÉ—u, É—aurin da aka yi masa ya kawo tabarbarewar rayuwar iyalinsa.
A ranar 29 ga watan Yuli 1966 Shugabannin sojojin Arewa sun yi nasarar yin juyin mulki na Ramuwar gayya a kan shugaban Najeriya mai ci Johnson Aguiyi-Ironsi, dan kabilar Igbo. An kashe Shugaban kasa Ironsi tare da kashe wasu Yarabawa da yawa. Banjo, dan kabilar Yarbawa, ya yi yunkurin kare wani jami’in soja bayarbe amma Olusegun Obasanjo ya kama shi ya jefa shi a kurkuku. Banjo ya bayyana cewa ba shi da laifi kuma an ki yi masa shari’a.
Biyafara da Mutuwa
Lokacin da aka shelanta kafa kasar Biyafara a ranar 30 ga Mayu, 1967 Shugaba Odumegwu Ojukwu ya saki Banjo daga gidan yari a Gabashin Najeriya ya nada shi matsayin Kanar a sojan Biyafara.
Lokacin da Sojojin Najeriya suka fara kaiwa kasar Biyafara farmaki a ranar 6 ga Yuli, 1967 Ojukwu ya tura Banjo da Manjo Albert Okonkwo su tunkari sojojin Najeriya. Banjo dai ya samu nasarar kwace garin Benin da cikin Tarayyar Najeriya kasa da kwana guda har ya samu shiga waje mai tazarar kilomita 300 daga babban birnin Najeriya Legas.
Bayan an fatattaki Banjo a yakin Ore, shi da wasu hafsoshi (Emmanuel Ifeajuna, Phillip Alale, da Sam Agbam) Ojukwu ya zarge su da laifin shirya masa juyin mulki. Bayan da aka yi musu shari’ar gaggawa da wasu marubuta suka bayyana a matsayin son zuciya. Banjo da wasu da ake zargi da aikata laifin zagon kasa an same su da laifin cin amanar kasa kuma aka yanke musu hukuncin kisa.
A ranar 22 ga Satumba, 1967 Banjo, Emmanuel Ifeajuna, da Philip Alale an kaisu tsakiyar birnin Enugu aka daure su a jikin dirka. Sojojin Biyafara suka harbe su. Lokacin da aka harbi Banjo, an ruwaito cewa ya yi kururuwa, "Ban mutu ba tukuna!" kuma sai an harbe shi sau da yawa kafin ya mutu.
Leave Comments
Post a Comment