Maganin mata — Abubuwan da suka dace kiyi amfani dasu kafin aurenki

Maganin mata — Abubuwan da suka dace kiyi amfani dasu kafin aurenki
Maganin mata 


Wannan rubutu shawara ce ga sisters masu shirin yin aure, wadanda aka kusa bikinsu.


Da yawan yanmata idan bikinsu ya kusa, ana fara gabatar musu da abubuwa iri-iri kamar maganin mata, aikinta kenan kwankwadar maganin karin ni'ima da dadi a shimfida. Amma ko kun san cewa wannan maganin matan yana da illa?


Illar budurwa ta dinga shan maganin mata da yawa kafin aure shine, wannan maganin yana chanja mata asalin dandanonta, ya kasance ta yi dadi fiye da misali, na san zaku ce to ai dama haka ake buƙata.


Matsalar shine, bayan wani lokaci, maganin zai sake ta, idan bata cigaba da sha ba, dadinta zai koma salaf kamar asalin yadda take, a lokacin shi kuma mijinta zai fahimci ta rage dadi, sai ya fara tunanin kara aure. Idan kuma ta ci gaba da shan maganin, za ta illata kanta, domin zai kasance ba za ta iya gamsar da mijinta ba sai ta sha maganin mata.


Da yawan maganin mata ana hadawa da chemicals, wadanda idan suka yi accumulating a jikin mace za su iya janyo mata cuta mai wahalar magani.


Yanzu menene mafita kan amfani da maganin mata don samun ɗanɗano?


Mafita shine mu koma asali, idan lokacin aurenki ya kusa, ki yi kokari sosai a wajen amfani da maganin infection. Duk wata lalura da kike fama dashi kamar basur, sanyi, da sauransu, ki yi kokari ki yi maganinsu. Duk wata mace mai lafiya to tana da ni'ima, amma shan maganin mata babu wani amfani da zai miki sai illa.


Abu na biyu, shine karin ni'ima ta hanyar natural sources, akwai nau'ikan abinci masu kara wa mace dandano da ni'ima, kamar irinsu dabino, aya, kwakwa, kankana, madara, zuma, da vegetables. Indai kina yawan cin abubuwan dana lissafo, kuna kina cin abinci mai gina jiki, to za ki yi dadi auntyna ba ruwanki da maganin mata.


Sannan ki dinga kokarin yin aikin motsa jiki koda a cikin gidane, kuma ki kasance mai tsafta. Waɗannan hanyoyin za su taimaka miki sosai wajen ƙara inganta lafiyar ki, da kuma jindadin zamantakewar aure tsakaninki da mijinki.


Insha Allah idan kika yi amfani da waɗannan shawarwari da muka baku za ku samu abinda kuke so, amma kada ku kuskura ku ce za ku yi amfani da maganin mata domin gyara jiki wajen ƙara ɗanɗanon jima'i ko niima. Allah Ya bada zaman lafiya.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post