Kada Ki Kuskura Ki Furtawa Mijinki Waɗannan Abubuwan A Duk Lokacin Da Ya Ɓata Miki Rai - Android Pols - latest news, natural remedies, and entertainment

Kada Ki Kuskura Ki Furtawa Mijinki Waɗannan Abubuwan A Duk Lokacin Da Ya Ɓata Miki Rai

Kada Ki Kuskura Ki Furtawa Mijinki Waɗannan Abubuwan A Duk Lokacin Da Ya Ɓata Miki Rai
Kada Ki Kuskura Ki Furtawa Mijinki Waɗannan Abubuwan A Duk Lokacin Da Ya Ɓata Miki Rai

 

Da yawan mata idan ransu ya ɓace sukan furta kalaman da duk ya fito daga bakin su na rashin daɗi ga duk wanda suka furtawa ba tare da sun yi tunani akai ba. Haka kuma ba kowace mace ta ke iya furta kalamai na hankali da nusutwa ba rai ya baci. Wanda kuma daga baya idan sun huce sai su zo suna nadama.


Yana da kyau a duk lokacin da ranki ya ɓaci ki ringa tunani kafin ki furta kalaman da za su jawo ki ɓata ran duk wanda kika furatwa su. A duk lokacin da mijinki ya ɓata miki rai ko kuma ya faɗamki wani abu na jin haushi to kada ki sake ki furta masa ɗaya daga cikin waɗanan Kalaman kamar haka.


(1) Faɗin Baƙar Magana Da Zagi;

Wasu matan idan ransu ya ɓaci suna da saurin yin zagi da faɗar baƙaƙen maganganu. Wasu har da furta kalaman irin su azzalumi, mugu, mara imani, mayaudari makaryaci, da dai sauran kalamai na cin mutunci. Furta irin wannan kalaman sun yi tsauri da yawa. Don haka idan ranki ya ɓaci ki tausasa kalaman da zasu fito daga bakin ki.


(2) Tsakanina Da Kai Allah Ya Isa;

Furta wannan kalmar shi ma babban kuskure ne, bai Kamata ki faɗawa mijinki irin wannan kalaman ba, a maimakon ki furta masa irin wannan kalmar sai kiyi amfani da salo na hankali kice idan nice na zalince ka Allah ya baiwa kowa haƙƙin sa. Domin Allah na baiwa wanda aka zalunta haƙƙin sa.


(3) Ba Zan Sake Amince Dakai Ba;

Furatawa miji irin waɗannan kalaman ba ƙaramin kuskure bane. A duk lokacin da kike so ki huce fushin ki to ba ta hanyar furta kalaman zagi za kiyi ba sai ki biyo ta hanya mai kyau kice bakiji daɗin abinda yai miji ba idan har kinyi hakan to zai ji aransa cewa yasan bai yi daidai ba.


(4) Ba Kada Gaskiya Ƙarya kake yi;

Mata sukan furta irin wannan kalaman ga mazajen su a lokacin da suke yin fushi. Su ma wannan kalaman suna da sauƙin faɗa wajen mata. Kisani cewa ba wai mijinki kaɗai ba ko da ɗan da kika haifa ne bai dace ki faɗamasa irin wannan kalaman ba balle kuma mijinki.


(5) Ai Laifin Ka Ne Ko Kuma Kaine Ka Jawo;

Koda mijinki ne da laifi kada ki furta masa hakan kai tsaye. Maimakon ki furta hakan kina iya cewa laifun mune duka. Idan har za ki furta masa cewa laifinka ne to akwai matsala. A maimakon ki furta masa hakan gara kiyi shiru domin ba shi wata damar wataƙila man gaba ya gyara kuskuren nasa.


Wannan sune kaɗan daga cikin kalmomin da mata suke furatawa mazajen su wanda hakan babbar matsala ce kuma suna tasiri a zuciyar duk wanda aka furtawa su ko da kuwa bayan komai ya wuce ne. Don mata ku Kiyaye kusan irin kalaman da za ku ringa bayyana wa mazajen ku su a lokacin da ranku ya ɓaci.


Related Posts:
Previous article
Next article

Leave Comments

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel