Kabarin Ibrahim bin Muhammad (SAW) Ɗan Manzon Allah (SAW) - Android Pols - latest news, natural remedies, and entertainment

Kabarin Ibrahim bin Muhammad (SAW) Ɗan Manzon Allah (SAW)

Kabarin Ibrahim bin Muhammad (SAW) Ɗan Manzon Allah (SAW)
Kabarin Ibrahim bin Muhammad (SAW) Ɗan Manzon Allah (SAW) 


Ibrahim رَضِيَ ٱللَّٰهُ عَنْهُ shi ne ɗan Annabi Muhammad ﷺ na uku da suka haifa tare da Mariya Qibtiya رضي الله عنها wadda ta kasance kuyanga. An ce Ibrahim رَضِيَ ٱللَّٰهُ عَنْهُ ya rasu ne a ranar 10 ga watan Rabi’ul Awwal kwana 2 gabanin wafatin Annabi Muhammad ﷺ. Ya rasu yana da shekaru 2.


Kamar yadda Ibn Kathir ya ruwaito daga Ibn Sa’ad ya ce an haifi Ibrahim (AS) ne a watan karshe na shekara ta 8 bayan hijira wanda yayi daidai da shekara ta 630 Miladiyya.


An radawa wa yaron suna Ibrahim, sunan Annabi Ibrahim (AS) Annabin da yazo a Littatafai Masu -Tsarki, wanda ake girmamawa a addinan Yahudanci, Kiristanci da Musulunci. An mika Ibrahim (AS ) a hannun wata mai suna Umm Sayf, matar Abu Sayf domin ta rene shi, wacce Annabi Muhammadu (SAW) ya ba wa akuya kyauta don ƙara sama mata madara. A lokacin da Ibrahim (AS) ya kamu da rashin lafiya, sai aka kai shi wata gonar dabino kusa da gidan mahaifiyarsa, domin ya sami kulawar mahaifiyar ta sa da yar'uwarta Sirin. 


Lokacin da aka bayyana cewa da wuya Ibrahim ya rayu, sai aka sanar da Annabi Muhammad (SAWW). Ya yi matukar kaduwa da wannan labarin, har ya ji guiwowinsa ba za su iya daukarsa ba. Nan da nan ya keta ta cikin gonaki ya isa wurin don yin bankwana da wannan jariri da ke shiri mutuwa a cinyar mahaifiyarsa. Annabi Muhammad (SAWW) ya dauki yaron ya kwantar da shi a cinyarsa yana girgiza hannunsa. 


Cikin tsananin damuwa ya ce wa dansa, “Ya Ibrahim, daga hukuncin Allah ne, ba za mu iya wadatar da kai da komai ba,” sannan ya yi shiru. Hawaye ne suke zubo daga idanuwansa. Yaron ya bude ido ya dube shi a hankali, mahaifiyarsa da yar'uwarta Sirin su na kallo su na kuka babu kakkautawa, Annabi bai umarce su da su daina kuka ba. Bayan wani lokaci sai Annabi Muhammad (SAWW) ya ce a lokacin "Idanuwansa na zubar da hawaye, kuma zuciya ta na cikin bakin ciki, amma ba za mu ce komai sai abin da Ubangijinmu ya amince, hakika ya Ibrahim, mun yi bakin ciki da tafiyarka daga gare mu."


Kusufin Rana

A cikin littafinsa Al-Bidaya wa-l-Nihaya, Ibn Kathir ya ambaci cewa Ibrahim ya rasu ne a ranar Alhamis 10 ga Rabi’ul Awwal shekaru 10 bayan hijira, kuma a wannan rana ta rasuwarsa ne aka yi kusufin rana. Saboda haka, wasu sun yi imanin cewa Allah yana nuna ta’aziyyarsa ga annabinsa ta hanyar lullube Rana. Annabi Muhammad (SAWW), ba ya son sahabbansa su fada cikin fitina ta hanyar wuce gona da iri akansa ko akan dansa, ya hau kan mumbarin masallaci ya ce, “Rana da wata ba sa husufi saboda mutuwa ko haihuwar wani. Duk lokacin da ku kaga kusufi kuyi salla kuma ku ambaci Allah. (Sahihul Bukhari 1043). (Bisa ga bayanan masu ilmin taurari na zamani, kusufin ranar ya faru a ranar 27 ga Janairu, 630 wanda aka gani a Madina).


Binnewa

An ruwaito Annabi Muhammad (SAWW) ya na sanar da Mariya da Sirin cewa Ibrahim zai samu mai renonsa a Aljanna. Litattafai daban-daban sun nuna cewa Umm Burdah, ko kuma al-Fadl ibn Abbas, daya daga cikinsu ne yayi wa Ibrahim wanka. Bayan haka, Annabi Muhammadu (Sallallahu), da kawunsa al-Abbas, da wasunsu suka ɗauke shi zuwa makabarta bayan sallar jana'izar da Annabi Muhammad (SAWW) ya jagoranta, an bunne shi a makabartar Al Baqi a Madina. Sai Annabi Muhammad (SAWW) ya cika kabarin da rairayi.


Related Posts:
Previous article
Next article

Leave Comments

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel