Ka San Sabubban Karkacewar Baki?
Ka San Sabubban Karkacewar Baki? |
Shanyewar ɓarin fuska larura ce da ke faruwa sakamakon lahani ga tushen jijiyar laka ta bakwai (7) a ƙwaƙwalwa ko kuma a hanyarta bayan ta fito daga ƙwaƙwalwa zuwa tsokokin fuska.
Wannan jijiyar laka na iya samun matsala kamar shaƙewa, dannewa, lahani daga harbin ƙwayoyin cuta ko kuma bugu daga waje a kan hanyarta daga ƙwaƙwalwa zuwa fuska domin kai saƙonni zuwa tsokokin ɓarin fuska, jakar yawu, jakar hawaye, tsinin harshe, da wata tsoka da ke dai-daita sauti da ke can cikin kunne, da dai sauransu. Idan ɗaya daga cikin waɗannan matsaloli ya faru, aikin jijiyar lakar zai yi sanyi ko rauni sai kuma ɓarin fuska ya shanye.
Yadda za a gane É“arin da fuska ta shanye
1) Karkacewar baki: wanda hakan zai sa wahalar rikewa ko zirarewar abinci ko abinsha daga baki.
2) Zubowar yawu ta É“arin da bakin ya shanye.
3) Sakkowar gira da kuma yawan zubar hawaye.
4) Gaza ko wahalar rufe ido.
5) Gaza ko wahalar bayyana labarin zuciya a fuska, kamar murmushi, fushi da sauransu.
6) Matsalar kasa É—aga gira ko tattare fatar goshi.
7) Ƙaruwar ƙara ko sauti a kunnen ta ɓarin da fuskar ta shanye.
8) Rashin jin É—anÉ—ano a tsinin harshe, da sauransu.
Abubuwan da ka iya janyo shanyewar É“arin fuska
1) Shanyewar É“arin jiki, wasu masu shanyewar É“arin jiki kan zo da shanyewar É“arin fuska.
2) ciwon siga.
3) Fashewar jijiyar jini a cikin kai.
4) Ciwon kunne.
5) Matsananciyar mura.
6) Bugu/rauni a kai ko fuska.
7) Doguwar tafiya a kan abin hawa tare da iska mai karfi na bugun É“arin fuska tsawon lokaci.
Wannan matsala ta shanyewar ɓarin fuska na ci wa masu fama da ita tuwo a ƙwarya, kama daga wahalhalu wajen cin abinci ko shan abinsha, zubar hawaye ko yawu wanda ke sa su jin kunyar bayyana fuskarsu a cikin jama'a, wanda hakan kan sa su ƙaurace wa jama'a, ko kuma tilasta musu rufe fuskarsu domin gudun tsangwama.
Wannan jinya ta shanyewar ɓarin fuska ana warkewa sarai kamar ba a yi ba. Don haka, idan kina / kana fama da wannan matsala tuntuɓi likitan fisiyo a asibiti mafi kusa da kai.
Likitan fisiyo na amfani da hanyoyin ƙwarewa domin yi wa jijiyar laka da tsokokin ɓarin fuskar ƙaimi domin farfaɗo da aikinsu.
©Physiotherapy Hausa
Leave Comments
Post a Comment