Jami'an Ƴan Sanda Sun Kame Wasu Mutane Da Suka Yi wa Mai POS Fashi Ciki Har Da Jami'an Soji Guda Biyu - Android Pols - latest news, natural remedies, and entertainment

Jami'an Ƴan Sanda Sun Kame Wasu Mutane Da Suka Yi wa Mai POS Fashi Ciki Har Da Jami'an Soji Guda Biyu

Jami'an Ƴan Sanda Sun Kame Wasu Mutane Da Suka Yi wa Mai POS Fashi Ciki Har Da Jami'an Soji Guda Biyu
Jami'an Ƴan Sanda Sun Kame Wasu Mutane Da Suka Yi wa Mai POS Fashi Ciki Har Da Jami'an Soji Guda Biyu

Yan sanda a jihar Borno sun kame wasu mutane da ake zargin su da yin fashi da makami, a cikin masu laifin da aka kama har da wasu jamian tsaro na soja su biyu. Kwamishinan ƴan sandan jihar Abdul Umar shine tabbatar da faruwar lamarin.


Waɗanda ake zargin an same su ne da yin fashi da makami a ranar 6 ga watan Fabrairu ga wani matashi mai sana'ar cire kuɗi ta POS mai suna Yusuf Usman wanda yake sana'ar  sa a kasuwar ƴan waya dake a Bulunkutu a birnin Maiduguri. 


A yayin kai harin ne dai ƴan fashin suka kashe wani mutum guda tare da raunata wani, amma jami'an na su sunyi nasarar kame mutane 3 waɗanda suka haɗa da Mustapha Lawan da ake yiwa laƙabi da Bakura Ɗan tawaye, sai Umar Ibrahim da kuma Abubakar Mohammed mai laƙabin Bro Shagi, a cewar Abdul Umar.


Ya bayyana cewa masu laifin da aka kame su dukkan su sun amsa laifin da ake zargin su da aikatawa, inda suka bayyana sunayen wasu mutane biyu daga cikin su cewa jami'an sojin Najeriya ne, cikin su akwai mai suna Pte Jibrin Adamu da kuma Lgogo Michael, wanda da su aka haɗa kai aka yi fashin. Kwamishinan yace za'a gudanar da bincike akan su daga nan kuma za mu gurfanar da su a gaban kotu domin yin hukunci.


A arewacin Najeriya dai sabon abu ne yiwa masu POS fashi, hakan ba kasafai yake faruwa a arewacin ƙasar ba sai dai a kudancin ƙasar. Sai dai kuma ana ɗora alhakin faruwar lamarin da rashin aikin yi da yai yawa a cikin al'umma, wasu kuwa na danganta shi da son zuciya irin na matasan. Wasu na ganin cewa ko da akwai matsalar rashin aikin yi ai ba kamata ka ɗauki abin wani ba.


Sai dai kuma abinda ya bada mamaki shine yadda aka ce an samu jami'an soji a cikin waɗanda aka kama da aikata laifin yin fashin. Sai dai ba'a gama bincike an tabbatar ba. Yanzu dai jama'a sun zuba ido domin ganin irin hukuncin da za'a yiwa waɗannan mutanen da aka kama da laifin yin fashi.


Related Posts:
Previous article
Next article

Leave Comments

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel