Ingantaccen Haɗin Namijin Goro Da Lemon Tsami |
A yau cikin ikon Allah mun zo muku da wani haɗi da zaku haɗa ku sha domin fitar da dukkan wasu abubuwa da suka shafi dattin ciki tare da ƙara kuzari da rage kiɓa da kuma yin maganin zazzaɓi mai zafi, ko kuma cutukan da ake ɗauka a wajen Ƙazanta da sauran su duka a cikin wannan haɗin da za kuyi.
Wannan haɗin an jarraba shi kuma anga amfanin sa ga jikin ɗan adam. Idan kunyi wannan haɗin Allah kaɗai yasan irin cutukan da zai yi muku maganin su da ƙwayoyin cutar da zasu narke a jikin ku. Shi wannan maganin garkuwa ne ga jikin ɗan adam idan mutum yana yin sa. Abubuwa 2 da za kuyi wannan haɗin da su.
Idan baku manta ba kwanakin baya munyi bayani akan amfanin da namijin goro yake yi da irin tasirin sa a jikin ɗan adam. Namijin goro aikin da yake yi a jiki ba za su lissafu ba saboda yawan su. To wannan haɗin ma dashi za kuyi za ku samu kamar guda 3 sai ku ɓare wannan ɓawon na jikinsa. Idan kun ɓare sai ku gurje shi ya zama gari.
Sai ku juye wannan garin namijin goro a kofi sannan sai ku samu lemon tsami ƙarami ku yanka shi gida 4 sai ku ɗauki ɗaya ku matse shi a cikin wannan garin namijin goron, idan kun matse lemon tsamin sai ku samu ruwan ɗumi. Sai ku ɗauko ruwan ɗumi madaidaici ku zuba a cikin garin namijin goron ku barshi yai kamar minti 15 zuwa 20.
sai ku shanye wannan ruwan, amma ana so ku haɗa wannan da safe domin da safe kafin aci komai ake sha. Duk wani abu da ya shafi dattin ƙirji da dattin mara, abinda ya shafi amosanin jiki da dukkan wata cuta da ba ku santa ba wannan haɗin zai yi muku maganin ta. Kullum kuyi shi ku sha har tsawon sati 1 ko kwana 10.
A kiyaye da abubuwan da muka lissafa za'a yi amfani dasu, namijin goron 3 ya wadatar shi kuwa lemon tsami 1 bisa 4 wato 1/4. Shi kuma ruwan ɗumin daidai gwargwado kada yai yawa kuma kada yai kaɗan. Idan kunyi za ku ga abinda zai faru da jikin ku cikin yardar Allah.