INA MASU NEMAN MATAN BANZA DA FASIKANCI? - Android Pols - latest news, natural remedies, and entertainment

INA MASU NEMAN MATAN BANZA DA FASIKANCI?

 


Shugaban Kasar Amurka Donald Trump ya sanya hannu a takarda domin tabbatar da ficewar Kasar Amurka daga cikin kungiyar kula da kiwon lafiya na Majalisar dinkin duniya wato World Health Organization (WHO)


Donald Trump yana ganin kungiyar WHO a matsayin wata kungiya da ake cuwa-cuwa da barnata da dukiyar Amurka a bisa tallafin da Kasar ke bayarwa na kudi da magunguna


Menene tasirin da wannan mataki da Donald Trump ya daukaka zai haifar ga duniya da sauran kasashe irin namu da suke samun tallafin magani daga WHO?


Allurar Polio zai hadu da cikas, yaki da zazzabin zicon sauro da sauran cututtuka da ake samun tallafin maganinsu daga WHO duk zai hadu da cikas


Naci karo da wani labari da na gani ana yadawa a group WhatsApp, ance Amurka ita ke bawa WHO tallafin maganin cutar kanjamau (HIV) wanda ake kaiwa Kasashen duniya a raba wa wadanda suka kamu da cutar HIV kyauta a Kasashen mu


Idan Amurka ta fice daga cikin WHO za'a dena bada maganin kyauta, duk wanda ya kamu da cutar HIV sai dai ya sayi maganin rage kaifin cutar da kudinsa, ance a duk karshen wata mutum zai kashe kudi dalar Amurka dubu biyu kimanin Naira miliyan uku da dubu dari uku wajen sayan maganin


Idan haka ya tabbata kunga ba kowa zai iya hlbiyan wannan kudi duk wata don ya samu maganin da zai rage masa tasirin cutar HIV a jikinsa ba, a kan hakane aka bawa masu neman matan banza shawara akan su tuba ko su tabbata suna amfani da abinda zai basu kariya daga kamuwa da cutar HIV


Yaa Allah Ka tsare mu daga kusantar kowani irin fasikanci


Related Posts:
Previous article
Next article

Leave Comments

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel