Illolin Talla Ga Rayuwar Ƴan Mata — Android Pols

Illolin Talla Ga Rayuwar Ƴan Mata — Android Pols
Illolin Talla Ga Rayuwar Ƴan Mata 



Shin kun san illolin talla ga rayuwar yan mata? Sana'ar talla tana da illoli masu ɗumbun yawa ga rayuwar mata musamman wanda ba su yi munzalin yin aure ba. 


A mafi akasarin garuruwan jihohin Arewacin Najeria, yana wuya kayi tafiyan minti guda baka ga ƴan mata suna talla akan titi, bakin kasuwa ko makaranta, tasha ko masana'anta, wuraren leburori, gidajen kallon kwallo ko sinima, filin kwallo da gidajen dambe, babu dare babu rana.


Babban abinda zai baka mamaki shine,y awancin abubuwan da suke sayarwa basa wuce abun Naira dubu daya ko dubu biyar, amma yarinya zata bar gidan iyayenta tun da safe har zuwa dare da sunan talla.


Mafi munin illolin talla ga rayuwar yan mata shine, wasunsu har lunguna suna shiga da ƙatti da sunan talla. 


Illolin talla ga rayuwar yan mata 


A dalilin talla ana samun abubuwa da dama musamman na ci gaban tattalin arziki, yana samar da kudin shiga sosai. Sai dai duk da haka masana sun bayyana yawan illar sa fiye da amfaninsa. Ga jerin illolin kamar haka;


"Talla yana kawo fyaɗe har ta kai ga taɓa mutuncin ƴa'ƴa mata. Wanda wannan shine babbar barazana da ƴan mata ke fuskanta. Domin kuwa akwai maza dake amfani da wannan dama idan mace na talla su yaudara ta su yi lalata da ita har su ɓata mata rayuwa.


"Talla tana hana ƴa'ƴa mata sallah a kan lokaci. Mafi akasarin yaran da zaka gansu suna talla a titi da lungu basu damu da yin sallah ba, da zarar sun bar gida babu ruwansu da yin wata ibada har sai sun koma gida sannan su haɗe sallolin da ba su yi ba. 


"Talla tana hana ƴa'ƴa mata karatun (addini ko boko). Wannan yana ɗaya daga cikin babbar illolin talla ga rayuwar ƴa mace, iyayensu basu damu su saka su makaranta ba domin ba za su iya ɗaukar ɗawainiyar tura su makaranta ba .


"Talla tana ɓata tarbiyyan ƴa'ƴa mata. Yawancin ƴan matan dake talla zaka samu an ɓata musu tarbiyya basu girmama mutane.


 "Talla ta saka ƴa'ƴa mata suna kamuwa da cututtuka masu hatsarin gaske. A dalilin talla an ɓata yara da dama ta hanyar yin lalata dasu tare da saka musu cututtuka. 


Waɗannan kaɗan ne daga cikin illolin talla ga rayuwar ƴan mata wanda ke jawo lalacewa da bata rayuwar su. Allah ka shiryar damu bakiɗaya. Allah Ya Wadatar Da Kowa Abinda Zai Ci .


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post