Illolin kwalliya ga yara — Android Pols - Android Pols - latest news, natural remedies, and entertainment

Illolin kwalliya ga yara — Android Pols

Illolin kwalliya ga yara — Android Pols
Illolin kwalliya ga yara 


Kwalliya ga yara mata abune mai qayatarwa da burgewa musamman idan anyi amfani da kaya masu kyau wurin yi.


Amma ya kamata iyaye mata su kula wurin sanin me ya kamata a ringa amfani dashi wurin shafawa fatar yara musamman jarirai ko masu qananun shekaru sosai.


Kayan kwalliya ko shafe-shafe da manya suke amfani dashi kamar su man shafawa, hoda, eyeshadow da makamantansu suna dauke da sinadaran da yayi wa fatar jariri qarfi domin dama ba don irinsu akayi ba.


Amma duk da haka  wasu hakan ba wani abun bane shafawa jariri ko yarinya mai qananun shekaru sosai su eyeshadow ko eyelashes, wasu ma har da qarin gashi ko kitso mai zafi da zai matse jijiyoyi sosai kamar yadda muke gani a wasu wuraren.


To manya ma ba ko wanne irin nau'in kayan ado ya kamata su ringa amfani dashi ba musamman masu larurar ido, ana basu shawarar daina amfani dasu dangin eyeshadow, eyelashes dasu mascara domin Illar da hakan yake dashi da lafiyar su. 


Ko nau'in mayukan shafawa na manya yanada qa'ida da irin nau'in mutanen da ya kamata su ringa amfani dashi,domin akwai kalolin fata da Allah ya hallici mutane dashi da yawa kamar :- 


-Oily skin 

-Dry skin 

-Normal skin 

-Combination 


Duk kayan shafawa a jiki na jarirai da yara qananu sosai  basa qunshe da sinadaran da zasu iya kawo matsaloli ga lafiyar su.


Ya kamata iyaye mata a kiyaye don Allah a haqura a bari sai sun girma suyi da kansu domin hadarin da hakan ke dashi ga lafiyar su.


Ko ba don kiyaye lafiya ba,ga masu qananun yara mata masu shekarun da basu zama cikakkun  mutane ba, wannan shafe-shafen bashida wani amfani musamman yadda al-amura suka canza yanzu Peadophile (wadanda aikata alfashar su akan yara sukeyi)sunyi yawa, qawata yara mata qananu da yi musu shafe-shafe wanda bai kamata ba yana kuma qara jan hankalin bata gari zuwa ga yaranku. 


Kubar yaranku suyi rayuwa irinta yarinta,idan lokacin adonsu yayi basai an musu ba zasuyi da kansu.


Allah ya kare mana zuri'ah daga mummunar qaddara, Ameen! 


Amb(Nr)Sumayya Ibrahim Sa'ad 

RN,RM, PND


Related Posts:
Previous article
Next article

Leave Comments

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel