Ilimin Da Suke Ƙunshe Cikin Mafarin Manhajar Koyon Likitancin — Android Pols
Ilimin Da Suke Ƙunshe Cikin Mafarin Manhajar Koyon Likitanci |
A shekarun farko na kwalejin Koyon Kiwon Lafiya ta Jami'a, akwai wasu ilimai da ke ƙunshe cikin manhajar domin samar da ingantaccen fandisho domin tunkarar koyon likitanci. Iliman sun haɗa da:
1. Anatomy = Kimiyyar sanin sassan jikin ɗan'adam filla-filla.
2. Physiology = Kimiyyar sanin ayyukan sassan jikin ɗan'adam.
3. Biochemistry = Kimiyyar sanin sauyawar ko sarrafuwar sinadaran ginin halitta.
4. Pharmacology = Kimiyyar ilimin magunguna.
5. Microbiology = Kimiyyar sanin ƙwayoyin cutuka
6. Pathology = Kimiyyar sani da gano cutuka.
7. Clinical Sociology = Kimiyyar ilimin zamantakewa a kiwon lafiya.
8. Clinical Psychology = Kimiyyar sanin sauyawar halayya da ɗabi'un ɗan'adam a kiwon lafiya.
9. Biostatistics = Kimiyyar ƙididdiga a kiwon lafiya.
10. Research = Koyon bincike da gudanar da shi a kiwon lafiya, da sauransu.
Bayan kammala fahimtar waɗannan ilimai, a shekaru na gaba za a keɓe ɗalibi da ilimin fanni ko ɓangaren da yake karanta kafin a yaye shi da digirin kiwon lafiya a jami'a.
© Physiotherapy Hausa
Leave Comments
Post a Comment