Idan Kuna Wanke Haƙoran Ku Da Wannan Sinadaran Zaku Kawar Da Dukkan Wani Dattin Baki — Android Pols

Idan Kuna Wanke Haƙoran Ku Da Wannan Sinadaran Zaku Kawar Da Dukkan Wani Dattin Baki
Idan Kuna Wanke Haƙoran Ku Da Wannan Sinadaran Zaku Kawar Da Dukkan Wani Dattin Baki


Yau a wannan filin zamu yi bayanine akan yadda zaku magnace matsalar dattin haƙora. Duba da irin tambayoyin da muke samu daga wajen masu bibiyar mu akan maganin da za suyi amfani dashi domin kawar da dattin haƙora. Shiyasa a yau muka shirya kawo muku wasu hanyoyi da za kuyi amfani dasu domin samun waraka daga wannan matsalar ta dattin haƙora.


Akwai waɗanda zaka ga haƙoran su sunyi gansa kuka, sai kaga haƙoran sunyi kamar wanda yake cin goro ko kuma shan sigari. Wato za kaga haƙoran sunyi wani kala sunyi datti babu kyan gani. Kuma mutane suna ƙorafin cewa suna gogewa ta hanyar yin amfani da man goge baki na bature amma kuma baya fita.


To ga dukkan waɗanda suke yi mana tambayoyi akan yadda za su magance wannan matsalar ga wasu abubuwa guda 3 da za kuyi amfani dasu domin ku magnace matsalar dattin haƙora. Duk yadda haƙori yakai da dafewa da yin tsatsa da kuma rashin haske. To kuyi amfani da wannan abubuwan da zan faɗa muku. Kuyi kamar Kwana 40 kuma amfani dasu  zakuga yadda haƙoran ku za su koma.


(1) Ku samu lemon tsami, kasami ƙarami guda 1 sai ka yanka shi ka matse ruwan a mazubi mai kyau.

(2) Citta Ɗanya wacce a turance ake kira da (ginger). Ka samu ka gurje ta a cikin abin magogi ko kuma ka daka ta.

(3) Gishir kamar rabin ƙaramin cokali ya wadatar.


Idan ka tanadi waɗannan abubuwan sai ka haɗasu waje guda ka cakuɗa. Ka tabbatar sun haɗe sun zama ɗaya. Sai ka samo wani abin wanke baki da ake Kiransa da colgate, zaku ganshi fari ne. Sai ka zuba kamar rabin cokali a cikin wannan haɗin cittar ka juya sosai.


Zaka dinga wanke bakin ka dashi sau uku a rana. Idan da safe ne kayi haɗin zaka wanke bakin ka dashi sannan da rana kayi da dare kafin ka kwanta bacci shima ka yi. A kullum haka zaka ringa yin haɗin kuna wanke bakin ku dashi. Kuyi haka har tsawon kwanaki 40 ko kuma 30.


Duk yadda haƙoran ka suka kai ga lalacewa ko kuma suka yi datti suka yi tsatsa suka yi duhu. Indai zaka juri yin wannan haɗin kuma kuna wanke bakin naku dashi a kullum to wallahi za kuga yadda haƙoran naku za suyi haske su fita. Idan baku samu farin colgate ɗin ba to zaku iya samun wani kamfanin amma ku samu wanda yake fari ne. Kuyi ƙoƙari ku gwada wannan domin mutane dayawa sun gwada kuma sunji daɗin sa.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post