HANYOYIN KULA DA KAI GA MASU ASTHMA — Android Pols - Android Pols - latest news, natural remedies, and entertainment

HANYOYIN KULA DA KAI GA MASU ASTHMA — Android Pols

HANYOYIN KULA DA KAI GA MASU ASTHMA — Android Pols
HANYOYIN KULA DA KAI GA MASU ASTHMA  


Shin kun san hanyoyin da za ku kula da kan ku idan kun kamu da ciwon asthama? Ga wasu daga cikin muhimman hanyoyin da za ku kula da lafiyar ku. 


HANYOYIN KULA DA KAI GA MASU ASTHMA 


-Gujewa fita waje lokacin yanayin sanyi ko qura.


-Tsaftace muhalli da cire su yana saboda qura.


-Neman shawarar masana kafin fara canja rayuwa irinta motsa jiki.


-Sanin abunda yake kuma tsananta ciwon domin guje masa.


-Yawaita cin kayan marmari domin bunqasa garkuwar jiki musamman bangaren kumburin huhu lokacin Inflammatory response.


-A yawaita shan ruwa sosai 


-A daina zama babu magani.


-Qauracewa kusantar dabbobi musamman ga wadanda hakan ke tayar musu da ciwon.


-A ringa qoqarin kaucewa saka sutura da zata matse jiki sosai musamman qirji ga mata.


-Idan magunguna sun qare ayi qoqarin zuwa asibiti domin sanin ko za'a iya ci gaba da amfani dasu ko ana buqatar canjawa.


-Ga masu sarari amfani da Humidifier a daki na taimakawa sosai wurin samar da iskar shaqa mai danshi ga huhu ba wacce ta bushe ba.


-Daukar matakin amfani da takunkumi duk lokacin da za'a shiga yanayin qura.


-A gujewa shiga cikin cunkoson jama'ah saboda qaranchin iska.


-Kula da kai daga kamuwa da duk wani ciwo mai alaqa da numfashi 


Allah ya bawa masu fama da larurar lafiya. Ameen!


Amb(Nr)Sumayya Ibrahim Sa'ad 

RN,RM,PND 



Related Posts:
Previous article
Next article

Leave Comments

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel