HANYOYIN KAMUWA DA CUTAR CIWON HANTA — Android Pols - Android Pols - latest news, natural remedies, and entertainment

HANYOYIN KAMUWA DA CUTAR CIWON HANTA — Android Pols

HANYOYIN KAMUWA DA CUTAR CIWON HANTA
HANYOYIN KAMUWA DA CUTAR CIWON HANTA


-Hepatitis A:- Gurbatuwar Abinci Ko Ruwan Sha Wanda Ya Gaurayu da Kashin Wani Mai Dauke da Cutar, Wanda Kwaruna (Flies) Ke Yadawa, da Kuma Hada Jiki (Body Contact) da Sauransu.


-Hepatitis B:- Idan Aka Sanyawa Mutum Jinin Mai Dauke da Ita (Transfusion of infected blood), Yin Amfani da Allura Ko Razor Masu Dauke da Kwayar Cutar (Use of infected sharp objects), Daga Uwa Zuwa Danta (Mother to Newborn), Lokacin Saduwa da Mai Dauke da Cutar (Sexual contact), da Sauransu.


-Hepatitis C:- Sanyawa Mutum Jinin Mai Dauke da Cutar (Transfusion of infected blood), Amfani da Allura Ko Razor Mai Dauke da Kwayar Cutar (Use of infected sharp objects), Musayar Abubuwan Tsafta Wanda Mutum Dayane Ya Kamata Yayi Amfani Dashi ( Sharing of personal hygiene implements), da sauransu.


YADDA AKE GANO CUTAR HANTA A JIKIN DAN ADAM


Ana Iya Gano Cutar Hepatitis (ciwon Hanta) Ne A Jikin Mutum Bayan Alamunta Sun Fara Bayyana, Daga Nan Sai Ayi Gwajin Jini Biyo Bayan Zukar Jinin Mutum.


YADDA AKE MAGANCE CUTAR HANTA HEPATITIS B


Maza garzaya asibiti mafi kusa da kai/ke don saduwa da ma’aikacin lafiya da darar ka/kin fara Jin alamomin dana ambata a sama.


HADURAN DAKE TATTARE DA CIWON HANTA 


Babban Hatsarin Dake Tattare da Wannan Cuta Shine; Hantar Mutum Zata Iya Lalacewa ta Yanda Dole sai Dai A Chanza Masa Wata, Idan Kuma back Allaah Ne Ya Kiyaye Ba to Mutum Na Iya Rasa Ransa.


YADDA AKE KARE JIKI DAGA FARUWAR CUTAR HANTA 


Ana Iya Kare Afkuwar Wannan Cutane ta Hanyar Yin Allurar Rigakafi. Hepatitis Vaccine sunan Allurar. Ita Kuma Ana Yiwa Mutum Ne da Zarar An Haifeshi, Sai Kuma A Sati Na Shida, Sati Na Goma, da Kuma Sati Na Goma sha Hudu da Haihuwar Jariri/Jaririya. A Dunkule Ana Kiran Alluran da Takwarorinsu da Suna “Pentavalent Vaccine”. Sai Kuma Inganta Tsaftar Jiki Data Muhalli, da Kuma Kiyaye Hanyoyin Kamuwa da Cutar.


Allaah Ya Kare Dukkanin Al’ummar Musulmi Daga Sharrin Wannan Cuta Amin.


Kabir Yusuf Danwurin Dutsi


Related Posts:
Previous article
Next article

Leave Comments

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel