Halayen Da Maza Suke Yi A Yayin Gudanar Da Jima'i Wanda Kuskure Ne - Android Pols - latest news, natural remedies, and entertainment

Halayen Da Maza Suke Yi A Yayin Gudanar Da Jima'i Wanda Kuskure Ne

Halayen Da Maza Suke Yi A Yayin Gudanar Da Jima'i Wanda Kuskure Ne
 Halayen Da Maza Suke Yi A Yayin Gudanar Da Jima'i Wanda Kuskure Ne


Akwai wasu halaye da yawancin maza suke yi a lokacin da suke saduwa da iyalin su wanda kuma hakan yakan gundurar matan su. Duk da yake ba duka ne matan suke iya fitowa su bayyana wa mazajen nasu cewa ba sa jindadin hakan ba.


Mata da yawa ba sa son irin wannan halayen da mazan suke nunawa amma ba duka matan bane sukan iya fitowa su nuna rashin jindaɗin su ba, game da irin wannan halayen da mazan nasu suke aikatawa ba a yayin jima'i ba. Kuma abin mamaki ma shine wasu mazan ma da yawa ba su san cewa hakan yana damun matan ba.


Shiyshaawarasa muka shirya kawo muku wasu daga cikin irin wannan kuskuren da mazan suke yi a yayin da suke gudanar da jima'i da iyalan su. Alwai su da yawa amma dai a wannan rubutun na yau za mu kawo muku kaɗan daga cikin kuskuren da magidanta suke aikatawa wanda kuma muke so su gyara.


Akwai abubuwan da yawa da mazan suke yi a yayin saduwa da iyalan su ga kaɗan daga ciki irin kuskuren kamar haka:


(1) Rashin Yin Wasanni;

Yawancin magidanta da sun zo yin jima'i da iyalan su ba sa iya yin wasanni na motsawa matan su sha'awa, abin haushi shine da miji ya zo sai ya haye matar sa ya yi abinda zai yi ya biyawa kansa buƙata ya tashi, ita kuma mace a wannan lokacin ne sha'awar ta take motsawa.


Wannan dabi'a da maza suke yi a lokacin saduwa da matan su yana matuƙar ɓatawa matan rai kuma yana saka su baƙin ciki. Don haka anan muna kira ga mazaje su sani cewa a duk lokacin da za su sadu da iyalan su yana da kyau su fara gabatar da wasanni kafin su sadu da su. Hakan zai sa su gamsu kuma buƙatar su ta biya.


(2) Ƙazanta Ko Rashin Tsabtace Jiki;

Da yawan maza ba sa tsaftace jikin su a lokacin da za su kusanci iyalan su. Abin mamaki sai kaga mutum ya fita tun safe yaje ya ɗauko rana, amma idan ya dawo gida ba zai yi wanka ya tsaftace jikin sa ya saka turare ba a haka zai afkawa matar sa yana tsami da warin rana.


Mata sun tsani maza masu irin wannan dabi'a. Yana da kyau a duk lokacin da za ka kusanci iyalan ka, yakamata ka tsaftace jikin ka kayi wanka kuma ka saka turare, kai kanka sai kafi jin daɗin kusantar ta kuma ita ma za taji daɗi ta gamsu. Kuma a wannan lokacin ana so ka yi amfani da turare iri na fata ba wanda ake sakawa a tufafi ba.


Indai zaka ringa yin wanka ka tsaftace jikin ka to tabbas za ka samu karin soyayya daga wajen matar ka, amma indai ba zaka ringa yin hakan ba, to kawai gwara ma ka haƙura da yin saduwar domin kuwa kana cutar da matar ka ne domin shi saduwa ba ta yin daɗi da gamsuwa idan wari yana tashi.


(3) Idan Ka Biyawa Kanka Buƙata Ka Tsaya Ita Ma Ta Kawo;

Ba duka ne maza suke iya yin hakan ba. Wasu mazan idan sun biya buƙatar su sai su tashi su rabu da mace. Ita kuma sha'awar ta ta na da yawa. Yana da kyau idan ka biya taka buƙatar to ka jira ta ita ma ta kawo. Shiyasa ake buƙatar a fara yin wasanni kafin akai ga yin jima'i domin a wannan wasannin ne mace za ta iya kawo wa na farko.


Wannan dai sune kadan daga cikin irin kurakuren da maza su ke aikatawa a yayin gudanar da jima'i da matan su. Da fatan maza za su fahimci irin wannan kuskuren da suke aikatawa kuma su gyara. Anan gaba za mu ƙara kawo muku wasu daga cikin wanda ba mu ambata a wannan rubutun ba.


Related Posts:
Previous article
Next article

Leave Comments

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel