Haɗin Shayin Maza Masu Saurin Kawo wa Da Kuma Maganin ƙanƙancewar Azzakari Da Ƙarancin Maniyyi
Haɗin Shayin Maza Masu Saurin Kawo wa Da Kuma Maganin ƙanƙancewar Azzakari Da Ƙarancin Maniyyi |
Wannan haɗin dai na maza ne kuma masu aure, idan kasan cewa kai gwauro ne ba kada mata to yin wannan haɗin ba naka bane. Shi dai wannan haɗin ta yana yin maganin abubuwa 3 ne kamar haka.
(1) Ƙarin Ruwan Maniyyi;
Shi wannan haɗin idan magidanci yai shi zai taimaka masa wajen ƙarin ruwan maniyyi, koda yanada shi to zai ƙaru idan yai amfani da wannan haɗin maganin.
(2) ƙarin Girman Azzakari;
Ga duk mutumin da yake fama da matsalar ƙanƙancewar Azzakarin sa, wanda gaban nasa yake zuƙewa yake komawa ciki to idan yai wannan haɗin zai taimaka masa wajen ƙara fito da gaban nasa yai ƙwari kuma yai girma Insha Allah.
(3) Saurin Inzali;
Duk mutumin da yake yin saurin inzali, wanda ba ya iya daɗewa tare da iyalin sa shima idan yai wannan haɗin zai samu sauyi cikin ƙaramin lokaci Insha Allah.
Sai dai shi wannan haɗin dabam yake da sauran irin haɗin maganin da muka bayar a kwanakin baya, domin shi wannan haɗin za ka yi amfani da shine a kullum har tsawon wata guda, domin ana so yabi jikin ka ne sosai yadda zai yi maka aiki. Ana so kullum kayi shi da safe kafin kaci komai ya zama na shine abinda zai fara shiga bakin ka.
Abubuwan da za'a samu domin yin wannan haɗin sune Kamar haka;
(1) Ɓawon Abarba; Idan aka samu Abarba kamar guda ɗaya to ɓawon ta shi ake da buƙata
(2) Namijin Goro; Ɗanye guda biyu shi za'a samu. Sai kuma
(3) Ɗanyar citta; ita ma za'a samu ɗanya babba guda ɗaya.
Wannan sune abubuwa 3 da ake da bukata domin yin wannan haɗin maganin. Idan ansamu ɓawon abarba sai a wanke shi a zuba shi a cikin tukunya, sannan sai a ɗauko ɗanyar citta a yanka ta ƙanana sai a zuba ta cikin tukunyar, shi ma namijin goro idan an cire ɓawon sai a yanka shi a zuba a tukunyar sa a zuba ruwa babban kofi ɗaya sannan a dafa.
Bayan kamar minti 10 zuwa 15 sai a sauke shi a tace sannan a samu lemon tsami guda ɗaya a matse shi a cikin wannan ruwan maganin da kuka dafa sai a shanye.
Ɗan uwa kayi ƙoƙari ka haɗa wannan maganin kasha mamaki, kuma wani abin birgewa da wannan haɗin yana da daɗin ɗanɗano a baki kuma zai yima magani da yawa a jikin ka. Ba kawai maganin gaban ka zai yi maka ba duk wata jojiya dake jikin ka ma zai zagaya. Indai kana yi zaka ga yadda gabanka zai yi ƙwari da kuzari.
Leave Comments
Post a Comment