Haɗin Ni'ima na Kankana Da Madara Domin Ma'aurata Zalla Banda Gwauraye - Android Pols - latest news, natural remedies, and entertainment

Haɗin Ni'ima na Kankana Da Madara Domin Ma'aurata Zalla Banda Gwauraye

Haɗin Kankana Da Madara Domin Ma'aurata Zalla Banda Gwauraye
Haɗin Ni'ima na Kankana Da Madara Domin Ma'aurata Zalla Banda Gwauraye 

A yau za mu yi bayani ne na musamman akan abinda ya shafi mata ko kuma ince ya shafi maza da mata gabaki ɗaya. Sai dai kuma matan su ne za su fi amafana daga wannan haɗin ni'ima. Sai dai kuma shi wannan haɗin idan mace za ta yi shi ana so ta tabbatar da cewa ta yi maganin sanyi a jikin ta.


Domin shi wannan haɗin ni'ima ne wanda idan kina da ciwon sanyi to ba lallai ne yai miki aiki ba. Amma idan kinsan cewa kina da matsalar sanyi to ki fara yi masa maganin sannan kuma sai ki fara shirin yin wannan haɗin. Haka shi ma duk namijin da yasan cewa yana da matsalar sanyi a jikin sa ko kuma ciwon siga shi ma ya fara yin maganin su kafin yai amfani da wannan haɗin.


Wannan Haɗin ni'ima ne yana da sauƙin haɗawa da kuma sauƙin sayen kayan da zaku haɗa shi. Abubuwan da za ku nema guda biyu ne kacal kamar haka;


(1) Kankana (watermelon) wanda masu iya magana suke yi mata laƙabi da uwar ruwa sai kuma na biyu shine 

(2) Madarar Gari (milk) amma ku samu original ba mara kyau ba.


Yadda za ku yi shine bayan kun samu wannan abubuwan guda biyu da muka ambata a sama, sai ku yanka kankanar ku daidai yadda zaku iya shanyewa kamar dai ta 100 ko 150 sai ku dake ta kuma ba'a cire ƙwallayen ta a haka zaku jajjaga ta kamar dai damun fura, sai ki ɗauko Madarar ki ta gari ki zuba ki juya ki yi bisimillah ki shanye. Wannan ga mace kenan.


Shi ma namiji idan zai yi zai iya dama ta kamar irin yadda mukai bayanin na mace ko kuma ya yayyanka ta ya ɗauko madarar ya barbaɗa a ciki sai ya ringa sha da cokali har ya shanye. Kuma ko da masu ciwon sanyi ne za su iya yin wannan haɗin ni'ima. Sai dai kuma ba zai daɗe yana aiki a jikin su ba.


Wannan haɗin idan an yi shi ba za ayi amfani da shi ba sai ya rage kamar saura minti 5 ko ƙasa da haka a fara saduwa Sannan za'a sha. Ku haɗa ku gani ku sha mamaki. Duk wanda yai wannan haɗin ko mace ko namiji za'a samu ni'ima sosai a yayin saduwar aure.


Related Posts:
Previous article
Next article

Leave Comments

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel