Haɗin Ni'ima, Idan Kinaso Ki Zama Cikakkiyar Mace To Ki Yawaita Yin Wannan Haɗin — Android Pols

Haɗin Ni'ima, Idan Kinaso Ki Zama Cikakkiyar Mace To Ki Yawaita Yin Wannan Haɗin
Haɗin Ni'ima


Duk macen da ke so ta dawwama cikin lafiya, haɗin ni'ima da aminci da ƙarko koda za ta kai shekaru 70 ko 80 ya zamana tana da inganci. Duk macen da take da rama a jikin ta ƙasusuwan jikin ta suka fito, duk macen da ta ke so fatar jikin ta ta ringa sheƙi tana laushi to ga wani haɗin ni'ima na musamman da zai taimaka miki wajen gyara miki jikin naki. Haka kuma masu fama da Zazzaɓi mai zafi da ciwon mara mai rikitarwa shima zai muku amfani.


Wannan wani haɗi ne wanda ba za mu iya kawo muku dukkan aikin da yake yi a jikin mace ba saboda amfanin da yake yi ba zai lissafu ba sai kin haɗa kinyi amfani dashi sannan zaki ga irin abubuwan da zai miki. Wannan haɗin yana aiki a jiki kamar wutar daji. Idan ya fara yi miki aiki a jikin ki yadda kika san kin kunna wutar gas haka zai ringa tafiya a jikin ki.


Wannan haɗin da za mu baku gwadajjene, sai kunyi zaku gane hakan. Kamar yadda na faɗa a farko matar da ke son girma da ƙwarin jikin ta da ƙwarin gaɓoɓi da ƙwarin ƙafafuwan ta da kuma lafiyar ta, ki ringa yin wannan haɗin kina shan sa da madarar shanu ko madara ruwa. Matar da take so ta tsufa da ni'ima a jikin ta koda ta tsufa to za ta samu kanta cikin ni'ima. Indai za ki jure kina yin wannan haɗin ni'ima to zaki mamaki.


Macen da take shayarwa idan tana fuskantar ƙarancin ruwan nono to itama idan za ta yi wannan haɗin tana sha to har tagama shayar da jaririn ba za ta samu matsala ba. Haka kuma macen da ta ke so ta ringa gamsar da maigidan ta wajen saduwar aure to kema ki ringa yin wannan kina sha. Shiyasa nace muku aikin da wannan sinadarin yake yi a jiki ba zan iya kawo muku dukkan su ba.


Wannan haɗin ba mai wahala bane, zaku nemi abubuwa guda 2 kawai. Ga su kamar haka;

(1) Garin Hulba, idan kunje Islamic chemist za su baku. 

(2) Madarar Ruwa, ko Madarar Shanu.


Idan zaki wannan haɗin kiyi shi da safe domin so ake yi kisha da safe da kuma dare. Zaki zuba ruwa kamar kofi 1 a cikin tukunya sannan ki zuba garin hulba kamar cikin cokali 2 sai ki tafasa su. Idan ya tafasa sai ki tace ki raba ruwan 2 ki samu abu mai kyau ki ajiye rabin, rabin kuma sai ki zuba madara shanu ko madara ta ruwa sannan ki shanye.


Ragowar rabin kuma za kiyi amfani dashi da dare shima sai ki zuba wannan madarar kodai da ta shanu ko kuma ta ruwa sai ki sha. Za kiga ikon Allah, Ki ringa yin sa a kullum idan kuma bakida halin yi kullum sai kiyi duk bayan kwana 2. Idan kinayi zaki rabu da waɗannan matsalolin da muka ambata. Sannan kuma haɗin ni'ima ne da zai taimaka miki ƙara samun ɗanɗano a yayin kwanciyar aure da mijinki. 



Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post