Haɗin Kankana Da Madara Da Yake Firgita Ma'aurata Wajen Saduwa — Android Pols
Haɗin Kankana Da Madara Da Yake Firgita Ma'aurata Wajen Saduwa |
Wannan haɗin gwadajjene kuma sahihi ne sai dai idan baki yi ba. Domin ni kaina ina amfana da wannan haɗin kuma na baiwa mutane da yawa sun gwada sun yi min godiya da addu'a saboda daɗin da suka ji. Indai batu ne akan ɗanɗano jima'i da juriya, wato Jindaɗi a yayin da ake jima'i. Domin duk saduwar da za'a yi tsakanin mata da miji idan babu daɗi da ɗanɗano to babu wani gamsuwa da za'a samu. Shi dai wannan haɗin da zan baku yana da matukar sauƙi wajen haɗawa.
Kuɗin ki ko kuɗin ka naira 200 kacal za ka yi amfani da ita ku sayi kayan haɗin, kuma ko ina kuke ana samun waɗannan kayan haɗin ko kana wata ƙasar ko kana birni ko kuma ƙauye ko kana gida ko kana kasuwa ko a makaranta kake zaka samu wannan abubuwan. Wallahi wannan haɗin yana yi daga yau ku fara yin amfani dashi kuga abin mamaki. Domin duk irin wannan abubuwan da kukeji muna kawo muku indai baku gwada ba to ba za kusan yanayi ko baya yi ba.
Ku samu kankana mai kyau wacce ta nuna tai jawur sai ku yanka ta, ku samu roba ƙarama ku yanka ta ƙananan. Amma kiyishi da yawa domin ke da maigida ne zaku sha kuma ana shan wannan haɗin ne kafin a kwanta bacci wato bayan sallah Isha idan anci abinci an ƙoshi sai a ɗauki wannan haɗin a shanye. Idan kin yanka wannan Kankana sai ki zuba madarar gari irin ta sachet a ciki son samu kuyi amfani da ta kamfanin peak domin tafi inganci.
Amma ba dole sai peak ba kowace iri indai ta sachet ce kuma ba ta lalace ba za ku iya yin amfani da ita, idan kin zuba madarar sai ki juya ta su haɗe da wannan Kankana. Idan kun gama cin abinci sai ku ɗauki cokali 2 ke da maigida kusha tare. Wannan haɗin a ranar da kuka haɗa kuka sha to za'a murje sosai akan gado kuma zaku fitar da ni'ima sosai. Don haka daga yau sai ku fara, idan da hali za ku iya yin sa a kullum kusha domin zai taimaka muku wajen ƙara muku ni'ima da samun gamsuwa.
Haka kuma idan kuna da hali zaku iya haɗa kankana da ayaba ku markaɗa su tare sai a zuba madara ta sachet kodai peak ko kuma wata daban sannan a haɗa da zuma kamar cokali 4 sai a juya sosai, zakuga ya canja kamanni ya koma kamar haɗin lemo to idan kunci abinci bayan minti 30 sai ku sha wannan haɗin tare. Ba zanyi wani dogon bayani anan ba domin duk abinda zance ba zai gamsar ba sai kun jarraba kungani.
Leave Comments
Post a Comment