Haɗin Gyaran Gashi Na Musamman Domin Mata — Android Pols

Haɗin Gyaran Gashi Na Musamman Domin Mata
 Haɗin Gyaran Gashi Na Musamman Domin Mata


Matsala ta gashi wanda mata ke yawan yin tamabya akan sa, kuma shi wannan matsala ta karyewar gashi da zubewar sa kamar yadda muka sha yin bayani tun a baya akwai abubuwa da yawa da suke haddasa shi kamar irin su amosanin wanda cutar sanyi ke kawo shi kamar, fitowar ƙuraje, da ƙaiƙayin kai wanda yawancin sakamakon amosanin ne.


Mata zakaji suna korafi akan cewa gashin kansu yana yankewa yana cirewa, to kamar yadda muka ce sanyi na amosani yana haifar da matsalar zubewar gashi amma kuma baya ga wannan akwai wasu dalilai kuma wanda ke jawo zubewar gashi kamar rashin tsafta. Rashin tsaftace kanki na daga cikin matsalar dake jawo zubewar gashi.


Wasu matan sai suyi wata ba su wanke gashin kansu ba, sai suyi kitso ya ɗauki tsawon lokaci babu tsifa wanda hakan ke sa datti ya taru kuma idan datti ya ƙaru to kuwa kwarkwata za ta nemi wajen zama a cikin gashin. Idan kuwa kwarkwata ta shiga to za ta jawo gashin ya fara karyewa kuma ya fara zubewa. 


Akwai wata mata da mukai magana da ita kwanakin baya tana cewa gashin kanta duk ya zube, wai tana so a bata magani domin gashin yadawo, tace tanayin wata 2 ba tare da ta wanke kanta ta ba. Kunga kuwa dole ne gashi yayi datti kuma idan yayi datti dole ƙwayoyin cuta su shiga su haifar da matsala. Don haka matakin farko dole ne sai kun kula da gyara gashin ku kuna wanke shi akai-akai.


Ga wasu abubuwa guda 2 da zaki amfani dasu domin dawo da gashin kanki. Su wannan abubuwan idan kin haɗa su zaki ringa wanke kanki dashi ki barshi tsawon minti 10 akan ki sai ki wanke. Daga baya kuma zaki iya amfani da man shampo na wanke kai domin gashin yai kyau.


Zaki samu albasa madaidaiciya ki yankata ki jajjaga ki matse ruwan sai ki ƙara ruwa kamar rabin ƙaramani kofi, zaki iya haɗawa da tafarnuwa sili ɗaya ki jajjaga sai ki tace ruwan ki zuba a wani kofin ki ajiye. Akwai mai na vasline sai ki zuba kamar cokali 2 ki haɗa da wannan ruwan albasar ki cakuɗa.


Zaki ringa ɗiban wannan ruwan alabasar da man Vaseline kina shafawa akan ki kina cakuɗawa yadda zai taɓa ko ina akan naki. Idan kin shafa zaki barshi tsawon minti 10 zuwa 20 sannan sai ki wanke. Amma kisani wannan haɗin na lokaci ɗaya ne gobe idan zaki ƙara yi sai dai ki kuma haɗa wani. Kiyi kamar sati 2 kina yin wannan haɗin kina shafe kanki dashi. 


Idan kinyi hakan zakiga yadda martabar gashin kanki zai dawo, duk wannan matsalar ta zubewar gashi zai daina kuma duk zakiga gashin yana ƙara fitowa sannan kuma zai yi laushi yai baƙi.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post