Haɗin Garin Ganyen Magarya Da Madara Domin Matan Da Sha'awar Su Ta Ɗauke — Android Pols

Ga Wani Haɗin Garin Ganyen Magarya Da Madara Domin Matan Da Sha'awar Su Ta Ɗauke
 Haɗin Garin Ganyen Magarya Da Madara Domin Matan Da Sha'awar Su Ta Ɗauke



Matsaloli da yawancin mata suke kuka akai, mata sunfi maza damuwa akan wannan matsala, wato matsalar ɗaukewar sha'awa da kuma gushewar ta. A shirye-shiryen mu da mukai a baya munyi bayani akan abubuwan da ke jawo ɗaukewar sha'awa da kuma gushewar ta gabaki ɗaya. Kamar yadda muka sha yin bayani wasu matan abinda ke jawo sha'awar su ta ɗauke halitta ce daga Allah, haka ya yi su duk maganin da za su sha ba za su samu yadda suke so ba.


Wasu kuwa sha'awar su tana ɗaukewa ne a dalilin samun cuta, kamar cutukan sanyi ko matsalar basir. Yawancin mata ba su san cewa basir yana yi musu illa ba, to kisani cewa basir yana kashe sha'awa ga mace. Cutar sanyi irin wanda ake ɗauka ta hanyar saduwa ko kuma ta wajen najasa idan kinyi tsuguno a wajen da yake mai datti ne to kina iya kamuwa da ciwon sanyi wanda zai iya gusar miki da sha'awa.


Akwai kuma yin wasa da al'aura wanda yawancin mata cikin kaso 90% cikin 100% ba su san irin illolin da yake haifar musu ba. Mun sha yin bayani akan adaina aikata wannan ɗabi'a ta yin wasa da al'aura domin tana jawo sha'awar mutum ta ɗauke gabaki ɗaya kuma tana jawo gaban mace ya ringa zubar da ruwa mai wari. Sannan kuma ya jawo ciwon jiki da gaɓoɓi da sauran cututtuka masu yawa. Don haka mata sai ku kiyaye.


Haɗin Garin Ganyen Magarya Da Madara Domin Matan Da Sha'awar Su Ta Ɗauke


Ga garin ganyen magarya da za kuyi amfani dashi domin dawo da sha'awar ku. Kamar dai yadda wasu suka sani ita magarya tana da ganye to shi za'a samu sai busar dashi idan ya bushe sai a daka shi a tankaɗe. Zaki ringa dafa shi kina tsarki dashi, zai sa miki sha'awa matuƙa dagaske. Shiyasa ma idan kinsan bakida miji kar kiyi tsarki da ruwan garin magarya, domin kuwa indai zaki amfani dashi sai ya motsa miki da sha'awa.


Hanya ta biyu kuma shine zaki ringa ɗiban garin ki zuba a kofi ki zuba madarar ruwa ko nonon saniya mai kyau ki shanye. Shima zaki ringa sha kamar sau 2 a rana safe da yamma. Zaki ringa jin sha'awar ki tana motsawa sosai. Shima wannan ba'a so macen da ba ta da aure ta ringa sha. Sannan kuma idan kina yin jinin al'ada kada kisha garin magarya da madara domin zai tada miki sha'awa saboda sinadaran dake jikin sa suna da ƙarfin gaske.


Idan kinyi kiyi ƙoƙarin sanarwar da abokiyar zaman ki itama ta yi, domin taimakon juna ne. Idan kuna yin wannan haɗin ba za ku ƙara neman wani maganin samun sha'awa ba domin wannan garin magarya kaɗai ya isheki zai yi miki komai.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post