Haɗin Budurwar Kaza Domin Matan Aure Da Kuma Amaren Da Za Su Yi Aure — Android Pols

Haɗin Budurwar Kaza Domin Matan Aure Da Kuma Amaren Da Za Su Yi Aure
Haɗin Budurwar Kaza Domin Matan Aure Da Kuma Amaren Da Za Su Yi Aure


Mata yau gare ku haɗin Kaza ne na musamman domin matan aure. Kuma shi wannan haɗin Idan kika yi shi zaki iya ɗaukar tsawon lokaci kamar wata 4 zuwa 6 yana yi miki aiki a jikin ki. Kuma wannan haɗin ba tare da kinsha wani maganin bature ko makamancin haka ba.


Yadda ake yin wannan haɗin kuwa shine,kaza za ki samu budurwa wacce ba ta fara yin ƙwai ba. Idan kin samu sai a yanka miki ita a gyara miki, amma ki faɗa musu kada su yayyanka miki ita. Idan ma zai yu kawai ki sa a gida a yanka miki ita ke sai kiyi gyaran ta da kanki.


Idan kin yanka kin fige gashin jikin ta sai ki yanke kan Da duburar ta. Sannan sai ki yanke mafitsara wato duburar ta sai ki kwaso kayan cikin ta wato su hanji da tumbi domin su ba'a buƙatar su. Amma kisani fa ba cikin ake yankawa ba iya duburar kawai zaki yanka ki cire kayan cikin.


Bayan haka sai ki wanke da ruwa duk dattin cikin ya fito. Sai ki tafasa kazar a wuta. Sannan sai ki ɗauko riɗi wanda aka fi sani da kantu kamar rabin gwangwani sai ki tafasa shi kaɗan. Sai ki juye shi a cikin duburar kazar ma'ana wajen da kika yanke kika zubar da kayan cikin.


Bayan haka sai ki ɗauko nonon raƙumi shima ki zuba a ciki sai ki zuba daidai misali ba wanda zai yi yawa ba. Sai ki ɗauko kayan miya da kika markaɗa ki zuba daidai misali ki haɗa da magi da mai sai ki samu zare ki ɗaure bakin zumɓutun kazar. Sai ki ɗora akan wuta ki barta ta dafu sosai. Amma ki tabbatar wannan kayan haɗin duk suna ciki.


Ƴar uwa kiyi ƙoƙari dan Allah ki Gwada wannan haɗin. Ga waɗanda su ka karanta wannan saƙon su yi ƙoƙarin sanarwa da sauran mata wannan sirrin. Duk wacce ta haɗa shi za ta yi mana godiya. Amma sai dai idan kinsan kina da ciwon sanyi kar kiyi wannan haɗin sai kin fara magance matsalar sanyin.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post