Hadarin Jirgin Saman Alhazai A Kano 1973 — Android Pols - Android Pols - latest news, natural remedies, and entertainment

Hadarin Jirgin Saman Alhazai A Kano 1973 — Android Pols

Hadarin Jirgin Saman Alhazai A Kano 1973 — Android Pols
 Hadarin Jirgin Saman Alhazai A Kano 1973 


A Rana Mai Kamar Ta Yau 22 Ga Watan Junairu 1973  Wani jirgi kirar Boeing 707 da aka yi hayarsa ya kama da wuta lokacin da ya ke sauka a filin jirgin saman Kano, Najeriya, in da ya kashe mutane 176 dake cikinsa.


Hadarin jirgin saman na Kano ya kasance jirgin fasinja Boeing (707) da aka yi haya a ranar (22) ga watan Janairun shekara ta alib (1973) wanda ya yi hadari yayin da yake kokarin sauka a Filin jirgin saman Kano. Wannan shi ne hadari mafi girma na jirgin sama da ya taba faruwa a Najeriya, yayin da fasinjoji (176) da ma'aikata suka halaka a cikin hadarin. Akwai (22) da suka tsira. Wannan da ya hada da matukin jirgin da ma'aikatan jirgin, bisa ga rahoton New York Times. 


Wannan shine hadarin jirgi mafi tayar da hankali zuwa lokacin. Gabanin 1973, jirgin kasar Rasha ne ya taba hadari inda mutane 176 suka hallaka. Jirgin mahajjatan mai kirar Boeing 707, mallakan kasar Jordan na daya daga cikin jiragen da ke jigilar mahajjatan Najeriya zuwa kasar Saudiyya a lokacin.


Rahotanni sun bayyana cewa jirgin ya kama da wuta ne yayinda ya nufi filin jirgin saman Kano. Amma dai ba a tabbata ko jirgin ya taba kasa ba a lokacin. 


Allah ya jikansu da rahama, ya karbi ibadarsu kuma ya kyautata makwancinsu.


Related Posts:
Previous article
Next article

Leave Comments

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel