Gidan Najeriya A Birnin New York Na Kasar Amurka — Android Pols
![]() |
Gidan Najeriya A Birnin New York Na Kasar Amurka |
Wannan dogon ginin da ku ke gani! Gidan Najeriya ne da aka kashe $ miliyan 32 wajen ginawa a gundumar Manhattan ta birnin New York na kasar Amurka, an gina gidan a karkashin gwamnatin Babangida. An bude ginin a shekarar 1993. Ginin yana dauke da ma'aikatun ofisoshin jakadancin Najeriya da kuma ofisoshin Majalisar Dinkin Duniya.
A watan Nuwamban 2013 an zargi gwamnatin Jonathan Gudluck da yunkurin siyar da ginin, amma gwamnatin ta fito fili ta musanta cewa tana shirin sayar da gidan.
An ce marigayi Firayi Ministan Najeriya, Sir Abubakar Tafawa Balewa ne ya siyawa Najeriya gidan a shekarar 1961 daga shahararren mai harkar gidaje John Davison Rockefeller kan kudi dalar Amurka miliyan daya. Gwamnatin Babbangida ce ta rushe tsohon ginin ta gina sabo kamar yadda kuke ganinsa a kuma aka sake bude shi a 1993. An ce wajen da aka gina gidan yana daya daga cikin wurare mafiya tsada a duniya.
Leave Comments
Post a Comment