Maganin ulcer sadidan |
Matsalar gyambon ciki wato ciwon ulcer. A baya mun kawo muku magunguna da dama na gyambon ciki wanda mutane da dama sun gwada kuma sunji daɗi ya yi musu aiki.
Yau ma ga wani sabon maganin ulcer da muka zo muku dashi da za ku hada kusha domin rabuwa da wannan ciwon na gyambon ciki (ulcer). Sai dai muna kara kira ga mutane da su daina yin amfani da abubuwan da suke jawo wannan ciwo na gyambon ciki (ulcer) wato abubuwan da idan anci su yake motsa wannan ciwon, amma idan aka bari aka sha magani za'a samu sauki daga wannan ciwo.
Wannan maganin ulcer za kuyi amfani da ganyen zogale. Shi dai wannan ganyen na zogale kusan kowa yasan shi domin ba mai tsada bane kuma ana samun sa a ko ina, Kuma babu inda ba'a yin amfani da wannan ganyen.
Yadda zaku haɗa maganin ulcer
Za'a samu ganyen idan danye ne sai ku ɗiba cikin hannun ku a samu ruwa cikin babban kofi a zuba sai a tafasa idan ya dafu sai a tace ruwan abar ruwan ya huce. Za ku raba ruwan biyu kusha rabi da safe rabi da yamma.
Idan za ku dinga yin hakan a kullum kuna sha na tsawon lokaci to indai matsala ce akan ciwon ciki, dattin ciki da duk wani ciwo da kuke ji a cikin ku zai yi muku maganin sa.
Indai ciwon gyambon ciki na damun ka to wannan ruwan na zogale zai taimaka maka kuma zai wanke maka dukkan wani datti dake a cikin ka. Idan ba ku samu danyen ganyen zogale ba sai ku samu busasshe ku daka shi ya zama gari ku dinga diba da cokali kuna dafa shi sai ku tace ku sha.
Hakika duk wanda zai juri yin wannan hadin maganin ulcer na dafaffen ruwan zogale yana sha to zai samu sauki daga ciwon gyambon ciki (ulcer) gabaki daya.
Da fatan za ku hada wannan magani ku yi amfani dashi. Kuma shi Shan ruwan zogale ba kawai sai wanda yake da ciwon gyambon ciki ne zai sha ba, yawan shansa a lokuta yana karawa mutum lafiya da inganta rayuwar sa.
ko likitoci sun yi fatawa akan maganin da ruwan zogale yake yi ga jikin dan adam. shiyasa ake so mata masu ciki su yawaita dafa ruwan zogale suna sha domin zai kara musu jini da lafiya.
Don haka kada ku yi sake da ganyen zogale domin yana magance cututtuka masu tarin yawa a jikin dan adam wanda ba za su lissafu ba.
Sannan Kuma yana kara inganta lafiyar duk mai yin amfani dashi. shiyasa kwararru suke baiwa masu fama da ciwon zazzabin typhoid da su dinga yawaita dafa ganyen suna shan ruwan sa domin yana magance zazzabin cizon sauro da na typhoid.