Ga Wani Haɗi Na Firgita Maigida Wanda Amarya Za Tayi Har Da Uwargida |
Wannan fa'ida ce da yakamata ace ko wace mace ta tsaya ta saurara kuma ta karanta. Kuma kamata yai duk wacce ta karanta ta bani tukici domin kuɗi ba za su iya biya ba. To amma dai zan baku shi kyauta cikin yardar Allah.
Duk macen da take so ta rikita maigidan ta ta hanashi sakat sai ya kusance ta. Indai kinyi wannan haɗin ko mota ko kuma aikin Hajj kikace maigida kina so to babu shakka zai yi miki ba tare da ɓata lokaci ba. Allah ya datar damu yasa abinda zamu faɗa ya amfanar damu baki ɗaya.
Hanyar da zaki bi domin yin wannan haɗin shine, idan kinje kasuwa ko kuma idan turawa kikai zaki samu dabino mai kyau. Za kuji muna yawan kawo fa'ida da dabino kunsan shi abu ne mai sirri da yake magance abubuwa da dama daga jikin ɗan adam sai dai ba kowane yasan hakan ba. Mu kanmu ba za mu iya faɗa muku adadin sirrin dake cikin dabino ba saboda ba za su lissafu ba.
Shiyasa yawancin haɗin magani za kuji ana a haɗa zuma da dabino da kaninfari da sauran su. Saboda sirrin dake cikin su Allah kaɗai yasani. Idan kin samu dabino sai ki samu kwakwa babba mai kyau, sai ki samu nonon raƙumi sannan kuma sai zuma.
Idan kin samu waɗannan abubuwan sai ki ɓare dabino ki cire ƙwallayen ki jiƙashi na kamar tsawon awa 1. Sannan sai ki fasa ɓawon kwakwar ki fasa ki haɗa da dabino ki markaɗa su sai ki samu mazubi mai kyau ki juye a ciki. Sannan ki ɗauko zuma kamar rabin kofi ki zuba a cikin wannan markadaɗɗen dabino da kwakwa. Shi ma nono raƙumi kamar kofi 1 sai ki ɗauko ki zuba shi a ciki.
Wannan haɗin idan kika yi shi zaki ringa sha kaɗan-kaɗan, ma'ana kisha kamar cokali 3 da safe 3 da dare kafin ki kwanta barci. Haka zaki ringa yi a kullum. Yawan adadin da kika haɗa yawan lokacin da zai ɗaukar miki kina amfani dashi. Idan kina da wajen ajiya mai sanyi zaki iya haɗa na tsawon sati guda kina amfani dashi.
Zaki iya yin wannan haɗin kamar sau biyar. Wato idan kinyi ya ƙare zaki iya maimaitawa har sau 5. Wannan shine tsumin amarya da uwargida. Amma asali dai haɗin na amarya ne ita ma wacce auren ta ya rage bai fi saura wata 1 ba sai ta fara yin wannan haɗin. Bayan kinje gidan mijin zaki cigaba da yin sa. Ana so idan kinci abinci sai kisha wannan haɗin. Amma ki ringa cin abinci mai lafiya.